Dortmund ta taka wa Barca burki bayan wasa 24 a jere ba a doke ta ba

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Borussia Dortmund ta taka wa Barcelona burki, bayan wasa 24 a jere ba tare da rashin nasara ba a dukkan kaka a bana.

Ƙungiyar Jamus ta doke da Sifaniya 3-1 a wasa na biyu a Champions League, zagayen kwata fainal da suka fafata a Jamus ranar Talata.

Duk da haka Barcelona ta kai daf da karshe a gasar zakarun Turai da cin 5-3 gida da waje, bayan da ta ci 4-0 a makon jiya a Sifaniya.

Serhou Guirassy ne ya ci wa Dortmund ƙwallo uku rigis, wanda ta farko a bugun fenariti, sannan ya kara biyu a zagaye na biyu da suka sha ruwa suka koma fili.

Barcelona ta zare daya ne ta hannun Ramy Bensebaini ɗan wasan Dortmund da ya ci gida.

Rabon da Barcelona ta yi rashin nasara tun cikin Disamba, bayan da Atletico Madrid ta ci 2-1, daga nan ta yi karawa 24 a jere ba tare da rashin nasara ba har da canjaras huɗu daga ciki.

Karo na uku kenan da suka fafata tsakanin Dortmunda da Barcelona a gasar zakarun Tutai a kakar nan.

Wannan shi ne karo na biyar da suka kece raini a tsakaninsu a Champions League, inda Barcelona ta ci wasa uku da canjaras ɗaya, Dortmund ta ci wasa ɗaya.

Kakakr 2024/2025

Champions League ranar Talata 15 ga watan Afirilun 2025

  • B Dortmund 3 - 1 Barcelona

Champions League ranar Laraba 9 ga watan Afirilun 2025

  • Barcelona 4 - 0 B Dortmund

Champions League ranar Laraba 11 ga watan Disambar 2024

  • B Dortmund 2 - 3 Barcelona

Kakar 2019/2020

Champions League ranar Laraba 27 ga watan Nuwambar 2019

  • Barcelona 3 - 1 B Dortmund

Champions League ranar Talata 17 ga watan Satumbar 2019

  • B Dortmund 0 - 0 Barcelona

Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu mai rike da kofin bara.

Dortmund tana mataki na takwas da maki 42 a teburin Bundesliga, bayan kammala wasannin mako na 29.

Barcelona za ta kara da Celta Vigo a La Liga ranar Asabar 19 ga watan Afirilu, ita kuwa Dortmund za ta fafata da Borussia Mönchengladbach ranar Lahadi a Bundesliga.

Ƴan Barcelona da suka je Dortmund

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Tuni kociyan Barcelona, Hansi Flick ya bayyana waɗanda ya je da su Jamus, domin fafatawa da Dortmunda a filinta na Signal Iduna Park.

Dani Olmo yana daga cikin waɗanda aka je da su Jamus, sai dai Alejandro Balde na jinya.

Cubarsí, R. Araujo, I. Martinez, Gavi, Ferran, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña, Pablo Torre da kuma Christensen

Sauran sun haɗa da Fermín, Pau Víctor, Lamine Yamal, Olmo, F. De Jong, Kounde, Eric, Szczęsny, Kochen, H. Fort da kuma Gerard Martín.