Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon kociyan Brazil Tite ya ɗauki hutu don kula da lafiyarsa
Tsohon kociyan Brazil, Tite ya ce ya ɗauki hutu daga harkokin tamaula nan take, domin ya kula da lafiyarsa.
Mai shekara 63 ya horar da Brazil tsakanin 2016 zuwa 2022, wanda ya lashe Copa America a 2019.
Tite, wanda aka kai asibiti a Agustan bara, saboda matsalar bugun zuciya, an yi ta alakanta shi da aikin kociyan, Corinthians, wadda ya hora karo uku.
Sai dai wasu rahotannin sun ce kociyan ya ji baya iya nunfashi yadda ya kamata da ciwon kai da jiri a washe garin da zai je Sao Paulo, domin rattaba kwantiragi.
''Na fahimci cewar akwai lokacin da ya kamata ka fahimci cewar a matakinka na mutum, rashin lafiya zai iya kamaka a kowanne lokaci.
''Ina mai matukar son ci gaba da abin da nake ƙaunar son yi, amma bayan da na tattauna da iyalai na, sun ce irin yanayin da nake ji ya kamata na huta, domin na kula da lafiya ta.
''Kamar yadda kowa ya sani na tattauna da Corinthians, amma dole ta sa na yanke shawarar hakura da karɓar aikin, domin lafiya ce kan gaba.''
Tite ya ajiye aikin horar da tawagar Brazil, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Croatia a bugun fenariti a gasar kofin duniya a Qatar a 2022 zagayen kwata fainal.
Daga nan ya koma Flamengo, wadda ta kore shi a Satumbar bara, bayan kaka ɗaya yana jan ragamar ƙungiyar.