Da ƙyar mu samu ƴan wasa a Janairu da za su bunkasa Arsenal - Arteta

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mikel Arteta ya ce da ƙyar ya samu ƴan wasan da zai ɗauka a Janairu da za su bunkasa ƙungiyar, wadda ke fatan kawo karshen kaka biyar rabon da ta lashe kofi.

Rashin fitatcen ɗan wasan da ke cin ƙwallaye ya sa Gunners ta yi rashin nasara a Emirates 2-0 a hannun Newcasle a League Cup wasan daf da karshe.

Har da wasan da Arsenal ta tashi 1-1 a gidan Brighton a Premier League, hakan ya kawo cikas a shirin da take na ɗaukar babban kofin tamaula na Ingila a bana.

Cikin kalubalen da Gunners ke fuskanta, Bukayo Saka zai ci gaba da jinya zuwa cikin watan Maris, kafin ya koma fagen fama.

Arsenal tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki shida tsakani da Liverpool mai jan ragama, mai kwantan wasa da Everton.

To sai dai Gunners tana da damar kai wa zagaye na biyu a Champions League na kakar nan kai tsaye.

Ranar Juma'a Arteta ya yi watsi da batun da ake cewar ya kamata ya ɗauko ɗan wasan gaba fitatce mai cin ƙwallaye a Janairun nan.

''Koda mun kawo ɗan wasa a yanzu babu abinda zai canja,'' in ji Arteta.

''Batu ne na ɗaukar wanda nan da nan zai bunkasa wasannin mu nan take a gurbin da muke bukata. Sai dai samo irin wannan ɗan ƙwallon a kasuwa a wannan lokacin zai yi wuya.

Ranar Lahadi, Arsenal za ta fafata da Manchester United a FA Cup, daga nan Gunners za ta yi karawa masu zafi.

Tottenham za ta ziyarci Arsenal a Emirates ranar 15 ga watan Janairu a Premier League, kwana uku tsakani Aston Villa ta kai mata ziyara a dai babbar gasar tamaula ta Ingila.

Daga nan Gunners ta yi wasa na huɗu a jere a gida da Dinamo Zagreb a Champions League ranar Laraba 22 ga watan Janairu.