Ancelotti zai bar Real Madrid domin karɓar aikin kociyan Brazil

Asalin hoton, Getty Images
Carlo Ancelotti zai bar aikin horar da Real Madrid a karshen kakar nan, domin ya karɓi aikin kociyan tawagar Brazil.
Mai shekara 65 ɗan kasar Italiya, zai zama kociyan Brazil daga 26 ga watan Mayu, da zarar an kammala wasannin La Liga na kakar nan.
Real Madrid, wadda take ta biyu a kan teburin kakar nan, za ta buga wasan karshe da Real Sociedad a Santiago Bernabeu ranar Lahadi 25 ga watan Mayu.
Zai bar Real Madrid a matakin ɗaya daga fitatcen kociyan da suka ja ragamr ƙungiyar a tarihi.
Ancelotti ya lashe kofi 15 a karo biyu da ya yi kocin Real Madrid, wanda a kakar bara ya ɗauki Champions League da La Liga.
Zai bar aikin horar da tamaula a Sifaniya, bayan da Barcelona ta doke Real Madrid 4-3 a El Clasico ranar Lahadi - kuma saura wasa uku a kammala kakar nan.
Wannan shi ne karon farko da Real Madrid za ta kare kakar bana ba tare da lashe kofi ba tun bayan shekara huɗu.
Tun kan fara kakar nan Real Madrid ta ɗauki Uefa Super Cup da kuma Fifa Inter Continental Cup.
Akwai karin bayanai........










