Ku San Malamanku tare da Sheikh Dan'azumi Musa Tafawa Ɓalewa

Ku San Malamanku tare da Sheikh Dan'azumi Musa Tafawa Ɓalewa
An wallafa

A shirin Ku San Malamanku na wannan mako, mun gabatar muku da Sheikh Dan'azumi Musa Tafawa Ɓalewa.

An haifi shehin malamin a 1953, a Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, ya fara karatun Ƙur'ani tun yana da shekara uku tun a gidansu.

Sannan ya shiga makarantar boko a garin Tafawa Ɓalewa, tun yana da shekara tara zuwa 10.

Bayan kammala furamare ya tafi garin Kano inda ya shiga makarantar sakandire a makarantar Sheikh Nasiru Kabara a Shahuci a birnin Kano.

Malamin ya yi digirinsa na farko a fannin Tarihi da addinin musulunci da kuma harshen Larabci a jami'ar Bayero ta Kano.

Ya kuma yi digirinsa na biyu a jami'ar Jos da ke jihar Plateau, yanzu haka kuma yana karatun diginsa na uku a jami'ar jihar Benue.

Manyan malaman da ya yi karatu a wajensu sun haɗa da Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Dahiru Bauchi da sheikh Ali tsafe.

Malamin ya ce ya je ƙasashe Irin Masar da Iraƙi da Senegal duk a harkokin karutun addini.

A yanzu haka Sheikh Dan'azumi shi ne shugaban majalisar Malamai ta ƙasa reshen jihar Bauchi, kuma mataimakin shugaban majalisar malamai ta ƙasar, kamar yadda ya bayyana.