Abinda ya kamata ku sani kan wasan Chelsea da Man City a Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Chelsea za ta karɓi bakuncin Manchester City a wasan makon farko a Premier League a Stamforrd Bridge ranar Lahadi.

Ƙungiyoyin sun kara sau uku a bara, inda suka tashi 4-4 a Premier League a Stamford Bridge da yin 1-1 a wasa na biyu a Etihad.

Sai dai City ta yi waje da Chelsea a FA Cup da cin 1-0 ranar 20 ga watan Afirilun 2024.

Wasannin da aka buga tsakanin Chelsea da Manchester City a 2023/24

English FA Cup Asabar 20 ga watan Afirilun 2024

  • Man City 1 - 0 Chelsea

Premier League Asabar 17 ga watan Afirilun 2024

  • Man City 1 - 1 Chelsea

Premier League Lahadi 12 ga watan Nuwambar 2023

  • Chelsea 4 - 4 Man City

Chelsea za ta buga wasan ba tare da Reece James ba, wanda aka dakatar ba zai buga wasa uku da fara kakar bana ba, sannan yana jinya.

Watakila Pedro Neto da Kiernan Dewsbury-Hall suna daga cikin waɗanda Chelsea ta ɗauka a bana da za su fara mata wasa a Stamford Bridge.

Manchester City za ta yi karawar ba tare da Rodri ba, wanda har yanzu ke jinya, wanda ya ji rauni a wasan karshe a Euro 2024.

Kociyan City, Pep Guardiola ya tabbatar da cewa Oscar Bobb zai yi jinyar mako uku, bayan da ya karya kafa a wajen atisaye.

Haka kuma da ƙyar ne idan Jack Grealish zai buga wasan, wanda bai samu buga Community Shield da City ta doke Manchester United a bugun fenariti ba.

Abinda ya kamata ku sani kan haɗuwa tsakaninsu

Chelsea ba ta yi nasara ba a karawa tara da ta fuskanci City a dukkan fafatawwa, tun bayan 1-0 da ta ci a Champions League a 2021, wadda ta yi canjaras biyu aka doke ta bakwai daga ciki.

Manchester City ta ci karawa uku da canjaras a wasa huɗu baya da je ta fafata a Stamford Bridge.

Chelsea

Chelsea ta kasa karewa a cikin ƴan huɗun farkon teburi a kaka biyu a jere a karon farko tun bayan 2002, inda ta kammala a mataki na 12.

Sai dai Chelsea ta haɗa maki 35 a 2024, waɗanda suka sha gabanta a haɗa maki a shekarar sun hada da Manchester City mai 51 da Arsenal mai 49 da kuma Liverpool mai 40.

Wasa biyu ne ta yi rashin nasara a karawar farko da fara Premier League a Stamford Bridge ta ci 12 da canjaras biyar tun bayan 3-2 da Burnley ta yi nasara a 2017.

Enzo Maresca shi ne na shida da zai ja ragamar Chelsea karkashin shugabancin Todd Boehly , tun bayan da ya mallaki ƙungiyar a Mayun 2022.

Cole Palmer shi ne kan gaba a Chelsea a Premier League a bara, wanda yake da hannun cin ƙwallo 22 da bayar da 11 aka zura a raga.

Manchester City

Manchester City ce mai rike da Premier League na bara, kuma na huɗu jimilla, wadda ta lashe Community Shield a watan nan.

City ta yi wasa 23 a jere a Premier League ba tare da rashin nasara ba, tun bayan da Aston Villa ta doke ta 1-0 a cikin watan Disamba.

Wannan shi ne karo na takwas a jere da City za ta fara wasan farko a Premier League a waje.

City ta lashe wasa 12 daga 13 a farkon fara Premier League, idan ka cire wanda Tottenham ta doke ta 1-0 a 2021-22.