Liverpool ta yi zarra a cinikin Guehi, Real Madrid na son Saliba

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta doke Chelsea da Newcastle United a farautar ɗan wasan Crystal Palace, Marc Guehi mai shekara 24. (Mirror)
Wakilin ɗan wasan gaba a Argentina Julian Alvarez ya ce Liverpool na son ɗan wasan mai shekara 25 tun kafin ya je Atletico Madrid daga Manchester City a karshen wancan kakar. (Winwin, via Liverpool Echo)
Liverpool za ta duba yiwuwar sayer da ɗan wasanta na Uruguay, Darwin Nunez a lokacin bazara, wanda kocin Arsenal Mikel Arteta ke kwaɗayi. (Fichajes - in Spanish)
Real Madrid za ta gwada sayan ɗan wasan Arsenal da Faransa, William Saliba mai shekara 23, a lokacin bazara. (Relevo - in Spanish)
Manchester United, Liverpool da West Ham na son ɗan wasan Lille mai shekara 25 daga Canada, Jonathan David, sai dai ƙungiyoyin na Firimiya za su fuskanci kalubale daga Barcelona da Juventus da Inter Milan. (Tuttojuve - in Italian)
Newcastle United da Aston Villa ke kan gaba a farautar ɗan wasan Besiktas mai shekara 19, Semih Kilicsoy, da Fulham da Everton da kuma Nottingham Forest ke zawarci. (Caughtoffside)
Sunderland za ta nemi sama da £20m kan ɗan wasanta na Ingila, Jobe Bellingham mai shekara 19, da Borussia Dortmund da Chelsea da Crystal Palace da kuma Tottenham ke son sayewa. (Football Insider)
Timo Werner mai shekara 29, zai iya komawa ƙungiyar New York Bulls a matsayin aro daga RB Leipzig bayan Tottenham ta nuna ba zata saye ɗan wasan na Jamus ba. (Teamtalk)
Mai buga gaba a Amurka, Christian Pulisic ya ce yana son ya cigaba da zama a AC Milan yayinda ake rade-radin kan ɗan wasan mai shkara 26 da ya sabunta yarjejeniyarsa da ƙungiyar ta Italiya.(Football Italia)
Kocin Liverpool Arne Slot ya kwaɗaita muradin saye mai tsaron ragar Brazil, Alisson Becker ɗan shekara 32. (Independent)











