Burina na kafa jami'a don marayu - Sa'a Dogon Bauchi

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama don kallon bidiyon
Burina na kafa jami'a don marayu - Sa'a Dogon Bauchi
An wallafa

Hajiya Sa'a Dogon Bauchi wadda kwamishina ce mai wakiltar shiyyar arewa maso yammacin Najeriya a hukumar Ƙidaya ta ƙasar, ta kwashe shekaru tana ayyukan tallafa wa marayu da marasa ƙarfi a yankin arewacin ƙasar mai fama da marasa galihu.

Hajiya Sa'a wadda ƴar asalin jihar Kaduna ce, ta ce "burina shi ne tallafa wa marayu su samu ilimi domin duk wanda ka bai wa ilimi to tamkar ka ba shi rayuwa a hannunsa."

Hajiya Sa'a tana aiwatar da irin waɗannan ayyukan na jin-ƙai ta hanyar gidauniyar da ta buɗe mai suna Sa'a Garba Dogon Bauchi Orphans Foundation.