Man city ta tsallake rijiya da baya a wasanta da Southampton

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta koma saman teburin gasar Firimiya ta Ingila bayan da ta yi nasara kan southampton da ci 1-0 a wasan mako na tara a da aka buga a filin wasan Etihad.

Erling Haaland ne ya zura ƙwallo a raga a mniti na biyar da fara wasa, da taimakon Matheus Nunes inda ya ci ƙwallonsa na 11 a kakar wasan bana.

Wannan sakamakon na nufin City ba ta yi rashin nasara ba a wasannin Firimiya guda 32 a jere tun bayan kashin da suka sha a hannun Aston Villa a ranar 6 ga watan disamban bara.

Southampton har yanzu tana tsaka mai wuya a gasar bana inda ta kasance kurar baya a teburi da maki ɗaya kacal.

Koci Russell Martin dai na fatan cewa mamallakan kulob ɗin za su yi haƙuri da shi yayin da ya ke ƙokarin farfaɗo da ƙungiyar bayan dawowarta gasar a kakar wasan bana.

Yadda wasa ta kaya a sauran wasannin Firimiyar Ingila

A sauran wasannin mako na tara na da aka fafata a filayen wasa daban daban na Ingila:

Aston Villa 1 AFC Bournemouth 1

Brighton 2 Wolverhampton Wanderers 2

Brentford 4 Ipswich Town 3

Everton 1 Fulham 1