Mbappe zai fara hutun dakatarwa a wasan Bilbao

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kylian Mbappe zai fara hutun dakatarwa wasa ɗaya ranar Lahadi a karawar La Liga da Real Madrid za ta yi da Athletic Bilbao a Santiago Bernabeu.

An bai wa Mbappe jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Antonio Blanco a wasan da Real ta ci Deportivo Alaves 1-0 a La Liga ranar Lahadi 13 ga watan Afirilu.

Wannan shi ne karon farko da aka bai wa Mbappe jan kati a Real Madrid tun bayan da ya koma can kan fara kakar nan daga Paris St Germain.

A rahoton da alkalin wasan ya rubuta ya ce ya kori Mbappe ne, saboda ketar da ya yi, wanda hukuncin zai kama daga dakatarwa wasa ɗaya zuwa uku.

An yi wa Mbappe sassaucin hukuncin, bayan da a rahoton alkalin wasan da ya rubuta ya ce ƙyaftin ɗin Faransa, ya yi kokarin taɓa ƙwallo ne.

Kenan Mbappe zai yi wa Real Madrid wasan karshe a Copa del Rey da Barcelona ranar 26 ga watan Afirilu, kafin nan Real za ta je Getafe ranar Laraba 23 ga watan nan.

Mbappe ya ci ƙwallo 33 a wasa 49 a dukkkan karawa a Real a bana, tun bayan da ya koma ƙungiyar kan fara kakar nan daga Paris St Germain.

Ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta ci karo da cikas a kakar nan, bayan da Arsenal ta yi waje da ita a Champions League da cin 5-1 gida da waje.

Real Madrid mai maki 68, wadda take ta biyun teburin La Liga za ta fafata da Bilbao a wasan mako na 33 ranar Lahadi.

Barcelona ce kan gaba a gasar La Liga ta kakar nan da maki 73, bayan cin Celta Vigo ranar Asabar 4-3 a karawar mako na 33.

Ƴan wasan Real da za su kara da Bilbao a La Liga

Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.

Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger da kuma Asencio.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Ceballos.

Masu cin ƙwalaye: Vini Jr., Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.