Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Harin Kuje alama ce ta gazawar gwamnati da kuma karfin ‘yan ta’adda a Najeriya’
Masana harkar tsaro a Najeriya sun bayyana harin da ‘yan kungiyar IS suka kai gidan yarin Kuje a matsayin alama ta gazawar gwamnati a kan tsaro.
Kazalika masanan sun kuma ce harin ‚yar manuniyace ta yadda ayyukan ‘ayn ta’adda ke kara karfi a Najeriyar.
Barrista Audu Bulama Bukarti, babban mai nazari a cibiyar Tony Blair da ke London, ya shaida wa BBC cewa, harin kuma wata alamace ta yadda ‘yan Boko Haram ke kara yaduwa da fadada.
Barista Bukarti, ya ce tun da aka kafa kungiyar Boko Haram ba a samu wani lokaci da ‘yan ta’addar suka je suka yi fito na fito da sojoji a wuri kamar Abuja ba sai lokacin da aka kai harin na Kuje.
Mai sharhin ya ce,” Gidan kurkukun da ‚yan IS din suka kai na Kuje, shi ne ake ganin ya fi kowane tsaro a kasar saboda a birnin tarayyar kasar ya ke”.
Ya ce to amma duk da haka ‘yan ta’addan sun yi nasarar kai harin har suka shafe sa’oi ana bata kashi da su daga bisani kuma suka kwashe mutanensu suka yi gaba da su.
Barista Bukarti, ya ce wannan manuniyace cewa ba in da a Najeriya ba a kai hari ba a yanzu.
Masanin tsaron ya ce,” Babbar damuwar ita ce a cikin gidan yarin na Kuje akwai manya-manyan shugabannin kungiyar ta Boko Haram da ke ciki, wanda kuma suka fi kowa hadari a cikinsu kuma a sakamakon harin an kubutar da su, a don haka akwai tashin sosai a kan hakan.”
Barista Bukarti, ya ce bisa la’akari da yadda aka shirya harin, hakan ya nuna cewa shiri ya kwancewa jami’an tsaron Najeriya, domin idan har akwai jami’an tsaro a kasa to bai kamata ace an kai hari irin wannan ba.
Masanin tsaron ya ce,” Babban tasirin da wannan harin zai iya yi ga Najeriyar ma shi ne an kunce manya-manyan kwamandojin Boko Haram wanda suke da gogewa, saboda haka kungiyar zata kara kaimi wajen kai hare-hare.”
A don haka wannan mummunan lamari ne musamman ganin cewa ita gwamnati bata daukar matakan da ya kamata a dauka, a don dole yanayi zai kara kazanta in ji shi.
Ya ce idan har gwamnatin tarayyar Najeriya bata dauki batun tsaro da muhimmanci ba kamar yadda ta dauki batun korona, to ko lallai akwai babbar matsala, in ji Bukarti.