Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan yadda aka yi yunkurin kashe Donald Trump a wurin yakin neman zabe
An fitar da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump daga wurin da yake gabatar da jawabi a wani taron yakin neman zabe a garin Butler na jihar Pensylvania da ke kasar Amurka.
Wani dan bindiga ne ya bude wa tsohon shugaban wuta daga kan rufin wani gini da ke kusa da wurin taron.
Dan takarar shugaban kasar na Jam’iyyar Republican ya duka zuwa kasa, yayin da za a iya ganin jini na zuba ta gefen fuskarsa.
Daga baya ya bayyana cewa ya ji gittawar harsashi ta kusa da fuskarsa, wanda ya shafi fatar kunnensa.
Lokacin da jami’an tsaron farin kaya suka mamaye dandamalin, Trump ya daga hannunsa sama yayin da ake sauka da shi daga kan dandamali.
Mahalarta taron su rika kwantawa a kasa yayin da karar bindiga ke tashi, yayin da wasu suka tsere.
Wani mutum da ke wurin ya shaida wa BBC cewa ya ga wani mutum a saman rufin wani gini dauke da bindiga jim kadan kafin ya fara harbi kan tsohon shugaban kasar.