Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ghana ta doke Mali a yunƙurin zuwa Kofin Duniya
Ghana ta doke Mali 2-1 a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka buga ranar Alhamis da dare.
Kamory Doumbia ne ya fara ci wa Mali ƙwallo ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, kafin Ernest Nuamah ya farke ta minti 13 da dawowa daga hutun.
Sai bayan minti huɗu da cikar lokaci tauraron ɗan wasa Jordan Ayew ya ci wa Ghana ƙwallon nasarar, abin da ya sa magoya baya ɓarkewa da sowar murna.
Sakamakon ya mayar da Ghana ta biyu a saman teburi da maki shida, yayin da Mali ke biye mata da maki huɗu. Sai kuma Comoros ta ɗaya mai maki shida kafin ta buga wasanta da Madagascar a yammacin yau.
Sai a ranar Litinin Ghana za ta karɓi baƙuncin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wasa na gaba a birnin Kumasi.