Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Roy Hodgson zai ci gaba da jan ragamar Crystal Palace
Crystal Palace ta tabbatar da cewa Roy Hodgson ne zai ci gaba da zama kocinta na kakar 2023-24.
Kocin mai shekara 75 ya koma ƙungiyar ne a watan Maris bayan ya maye Patrick Viera da ya yi domin jan ragamar ƙungiyar zuwa ƙarshen kakar da ta gabata.
Ya taimaka wajen ceto ƙungiyar daga faɗawa rukunin ƙarshe na Premier ya samu maki 18 a wasa 10 da ya buga inda ya kammala a matsayi na 11.
Hodgson ya ce ya "matuƙar jin dadi da alfaharin zamansa a ƙungiyar " ta Crystal Palace.
Hodgson ya share shekara huɗu a ƙungiyar zuwa 2017 kuma ya yanke shawarar ya ajiye aikinsa, ya hakura da harkokin kwallon ƙafa a 2021.
Tsohon kocin Ingilan ya zama kocin Watford a watan Janairun 2022 amma ya bar ƙungiyar watanni biyar baya yabar ƙungiyar saboda fadawa Championship da ta yi.
Sai da ƙungiyar ta yi wasa 12 a duka gasar da ta ke yi ba tare da ta yi nasara ba a lokacin da Viera ke jan ragama, kafin Hodgson ya koma ƙungiyarsa ta yarinta ya cece ta.
Ya shafe sama da shekara 45 yana koci, inda ya koyar da ƙungiyoyi irinsu Inter Milan da Blackburn Rovers da Fulham da Liverpool da kuma West Brom, ya kuma ja ragamar tawagar Switzerland da United Arab Emirates sai kuma Finland.