Matakan magance lalular tankwashewar tafin kafa

An wallafa

A farkon wannan shekarar, Serigne, mai shekaru 14, ya sakankance cewa ba zai kara fita daga gidansu ba. Yana iya tafiya a hankali bayan da aka haife shi da wata lalura da tafin kafafunsa biyu ke kallon ciki.

Yana jin kunyar fita waje, sakamakon yadda wasu ke tsokanarsa ta hanyar kwaikwayon tafiyarsa, wasu kuma na kiransa da sunaye iri-iri na tsokana.

Amma a yanzu cikin kasa da wata shida an yi masa tiyata domin gyara masa kafafuwan nasa, kuma a halin yanzu mafarkinsa na buga wa kasarsa Senegal wasa kwallon kafa na iya tabbata.

Serigne na da lalaurar takwashewar tafin kafa, kuma a yanzu za a shiga wani mataki a gyaran kafafun da ake masa.

A cewar gidauniyar Miraclefeet,  kowacce shekara ana haifar jarirai 200,000 da lalurar tankwashewar tafin kafa, kuma daga cikin mutum kusan miliyan 10 da ke rayuwa da lalurar a kusan miliyan takwas ba su taba samun magani ba.

A baya-bayan nan Senegal ta bi sahun wasu kasashen Afirka wajen fara amfani da hanyar Ponseti wajen gyara wannan lalura.

Ponseti hanya ce ta farko ta gyaran kafar da aka sa wa sunan wani likitan Sifaniya wanda shi ne ya kirkiro aikin .

Wannan na nufin likitocin Senegal sun kware wajen sanin yadda ake wannan aiki, kuma yanzu suna amfani da ita wajen yi wa  matasa da manya aiki domin warkar da su.

Mahaifiyar Serigne na farin ciki samun saukin da danta ke yi. Ta fi kowa sanin irin wahalar da ya sha sakamakon wannan lalura.

“Akwai wani lokacin da ya kasa fita daga gida tsawon kwana uku, na ji takaicin hakan sosai, amma yanzu muna jin dadi.”

Daga cikin matakan da ake bi na yin aikin gyaran, a kowane makon akan sake wa kafar bandejin da ake nadeta da shi domin ta rika sauyawa zuwa yadda ake bukata sannu a hankali.

To amma sakamakon yadda lalurarsa ta tsananta, an sake masa bandejin da ake nade kafafun nasa da shi kusan sau 20 a cikin makonni biyar zuwa takwas.

A karshen kowane aiki ana bukatar yi wa mutum aikin tiyata a kafar tasa domin cire wasu abubuwa, in ba haka ba kuwa aikin ba zai yi kyau ba.

A ‘yan kwanakin da suka gabata aka saka wa Serigne bandejin karshe a aikin da ake yi masa.

Bayan haka yana bukatar a yi masa tiyata a kafafaun nasa domin taimaka masa koyon yadda zai yi tafiya bayan da kafafun suka yi nauyi, kuma yana bukatar a daura masa wata safa a kafafunsa domin taimakawa wajen daidaita kafafuwan nasa, amma bisa ga alama aikin na tafiya yadda ya kamata.

Fatou wata yarinya ce da ake yi wa aikin gyaran kafafun a wani asibiti a birnin Dakar bayan ta shafe tafiya mai nisa kafin ta zo wannan asibitin, a lokacin da a yau take cika shekara 13 da haihuwa a yau din ne kuma ake cire mata bandeji na hudu a aikin da ake yi mata.

A lokacin da mai aikin jinyar ke cire mata bandejin daga kafafun nata, Fatou ta janye kafar saboda ciwo, to amma sai ma’aikaciyar jinyar ta rarrashe ta domin ta samu nutsuwa.

Ma’aikaciyar jinyar ta shaida wa BBC cewa "mun yi imanin cewa za ta warke kuma za ta taka kafarta yadda kowa ke takawa’’ ta fada cikin murmushi.

Fatou ta shaida mana cewa ba ta yi tsammanin za ta warke ba kasancewa tana rayuwa a yankin karkara a kasar, dan haka yanzu tana murna da wannan aiki.

Zuwa makaranta  ya yi mata wahala, tana kallon ‘yan uwanta yara suna tsalle da gudu, inda ita kuma take dogara da sandunan guragu.

"Akwai abubuwa da dama da nake son yi, amma bana iya yinsu, amma idan na warke zan yi duk abinda nake son yi’’. Daga ciki akwai babban burinta na zama likita.

To amma ba kowa ba ne ya samu wannan dama ta aikin gyaran kafar, alal misali Oumou Barry mai shekara 32, ta nuna mana kafarta a lokacin da muka ziyarce ta a unguwar Lac Rose da ke binin Dakar, kafar tata ta yi girma tare da lankwashewa sosai.

Ta yi kokarin takawa da kafar amma sai ta yi ihu sakamakon zafin radadin ciwon da kafar ke yi, abinda ke nuna cewa ba za ta iya tafiya mai isa ba.

‘’A lokacin da nake yarinya, rayuwata ta kasance cikin tsangwama saboda wannan lalura’’ ta fada a yayin da take share hawaye.

''Nakan tambayi mahaifiyata cewa me yasa nake haka? Ita kuma takan amsa min da cewa haka Allah ya halicceni kuma a haka aka haifo ni''.

Ta ce lokaci mafi tsanani a gareta shi ne a lokacin da ta fara zama budurwa a lokacin da kawayenta suka fara sanya takalma na kwalliya ita kuma ta ci gaba da saka sandal, daga karshe ta ce dole ta daina zuwa makaranta saboda ba za ta iya jure tsangwamar da take fusktanta ba.

Bayan da ta rabu da kawayenta na makaranta ta fara sana’ar kitso to amma daga baya ta daina wannan sana’a.

Oumou ta yi aure kuma a yanzu tana da ‘ya’ya biyu dan haka rayuwarta ba ta cikin tsangwama kamar sauran masu lalura irin nata, amma duk da haka tana jin zafin wannan lalura kasancewar ba ta yi karatu ba balle ta samu aikin gwamnati.

Sakamakon yawan shekaru da Oumou ke da su ba za a iya yi mata aikin Ponseti na gyaran wannan laulura ba, kasancewar aikin baya yin kyau ga mafiya yawan mutanen da suka manyanta.

Duk da cewa kawo yanzu babu wani bincike a kimiyance da yake nuna musabbabin haihuwar mutum da wannan lalulura, bincike ya nuna an fi haifar maza da lalurar fiye da mata.

Kuma mafiya yawan mutanen da ke dauke da wannan lalura suna kasashe matalauta ne watakila sakamakon yawan yawan haihuwa da ake samu a irin wadannan kasashe, kuma a irin wadannan kasashen ne ba a iya magance wannan lalura.

Aisha Mballo  wata mace ce guda daya da ta sadaukar ta rayuwarta wajen ganin cewa an yi wa masu irin wannan lalurar aiki tun suna kanana.

A lokacin da muka hadu da ita, tana tafiya cikin nutsuwa da kwarin jiki a cikin kasuwar garin Thies rike da katon littafin hotuna.

Littafin na bayani ne kan yadda ake maganace wannan lalura ta hanyar aikin da ke kira Ponseti, ta zo nan ne domin binciko masu irin wannan lalura domin taimaka musu da shawarwari.

Aisha ta ce ita ma da haka kafafunta suke, sai a wajen shekarun 1990 a lokacin tana budurwa aka yi mata aikin gyaran kafafun a Amurka.

A yanzu tana aikin sa kai a matsayin jakadiyar gidauniyar MiracleFeet mai fafutikar ganin an kawar da wannan lalura.

Aisha ta ce ‘’Idan mutane suka fahimci cewa ‘ya’yansu na dauke da wannan lalura, to kar su boye yaran a gida, su kawo mana su, mu kuma za mu kai su asibiti domin a yi musu aiki’’.

Rosalind Owen na kungiyar yaki da lalurar tankwashewar tafin kafa ta duniya wanda ya yi nazari kan yadda ‘yan Afirka ke kallon wannan lalura ya ce a wasu garuruwan Afirka masu dauke da cutar na fama da ‘’matsaloli na tsangwama’’.

"Mutane na tunanin cewa masu irin wannan lalura wani laifi suka yi wa Ubangiji ya halicce su a haka, ko kuma an yi wa mai laluar tsafi ne ya sa ya zama haka ko kuma wai iyayensa ne suka aikata wani laifi’’.

A yayin da yanzu a Senegal kusan kashi 20 cikin dari na masu irin wannan lalura ake magance musu ita tun a lokacin haihuwa, a yanzu ana samun ci gaba sosai a yakin da ake yin a kawar da lalurar.

Kafin wakilan BBC su bar garin na Thies sun ziyarci wajen asibiti domin ganin wata jaririya ‘yar mako biyu wadda aka saka wa sabon bandeji a kafarta.

Likitoci da masu aikin jinya na kokarin nade siraran kafafuwanta da bandeji.

Wannan shi ne lokacin da ya dace na magance wannan lalura.