Za mu ci gaba da sa ƙwazo har zuwa karshen kakar nan - Walker

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙyaftin, Walker ya sanar da magoya bayan Manchester City cewar za su ci gaba da sa ƙwazo a wasannin gaba har zuwa karshen kakar nan.

City ita ce ke rike da kofin Premier League na bara, amma yanzu tana fuskantar kalubale a dukkan karawar da take yi.

Mai tsaron bayan tawagar Ingila ya bayar da gudunmuwar da City ta lashe Premier League huɗu baya da Champions League da League Cup da FA Cup da Club World Cup.

Sai dai a ranar Lahadi, City ta yi rashin nasara a gidan Liverpool da ci 2-0 a Premier League, karo na shida a jere da aka doke ta, kuma wasa na bakwai a jere ba ta yi nasara ba.

Ƙungiyar Etihad ta yi kasa zuwa mataki na biyar a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki 11 tsakaninta da Liverpool mai jan ragama.

Walker ya sanar a shafinsa na sada zumunta cewar ''Mun lashe kofi a ranar karshen gasa karo da yawa, mun kafa tarihin haɗa maki sama da 100.

''Karo da yawa mun ƙware wajen shawo kan kalubale, kuma za mu kara sa ƙwazo. Ina muku alkawarincewar za mu ci gaba da kokari har zuwa karshen kakar bana.''

City ta zura ƙwallo 3-0 a ragar Fayenoord a Champions League a makon jiya daga baya aka farke su saura minti 15 a tashi daga karawar a Etihad.

Ranar Laraba Nottingham Forest za ta ziyarci City, domin buga Premier League a Etihad, idan ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta yi rashin nasara za ta kara yin kasa a teburi.