Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi waje da su Messi a zagayen farko a MLS Cup
Lionel Messi ya ci ƙwallo, amma bai hana Inter Miami ban kwana da MLS Cup ba a karawar cike gurbi da suka yi da Atlanta United.
Atlanta United ta yi nasarar cin 3-2 a fafatawar da suka yi Fort Lauderdale a birnin Florida, tun kan nan kowacce ta yi nasara a wasa ɗaya.
Miami ta samu gurbun shiga gasar ne, bayan da ta haɗa maki 74 daga karawa 34 a shiyyar yammaci, wadda ta lashe kyautar garkuwar magoya baya.
Miami ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Matias a wasan da suka yi a Chase Stadiya daga nan Atlanta ta zura biyu a raga cikin minti biyu ta hannun Jamal Thiare.
Daga baya ne Atlanta ta kara na uku ta hannun Bartosz Slisz daf a tashi karawar, Inter ta yi korafin ya kamata a dakatar da wasan bayan da mai tsaron baya, Tomas Aviles ke kwance a kasa sakamakon rauni.
A watan jiya aka bayyana Inter Miami cikin ƙungiya 32 da za su buga Fifa Club Cup a baɗi, gasar da aka kara yawan waɗanda za su fafata a wasannin.
Cikin watan Disamba Miami ta dauƙi ɗan wasan Uruguay, Luis Suarez, domin ya sake buga tamaula da Messi tare da Sergio Busquets da kuma Jordi Alba.
Atlanta za ta fuskanci Orlando City, yayin da New York City za ta fafata da New York Red Bull a wasan daf da karshe, inda za a yi karawa ɗaya maimakon ukun da aka tsara.