Kalli hotunan ziyarar Firaministan Indiya a Najeriya

Firaiministan Indiya, Narendra Modi da shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Asalin hoton, X/Bola Tinubu

Bayanan hoto, A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba ne Firaiministan Indiya, Narendra Modi ya isa Najeriya domin wata ziyara da ya kai a ƙasar.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2
Lokacin da Narenra Modi ya isa birnin Abuja

Asalin hoton, X/Narendra Modi

Bayanan hoto, Ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu jami'an gwamnati ne suka tarbi shugaban a filin jirgin sama na Abuja kuma ya samu tarba ta tarba ta masu kaɗe-kaɗe da raye-raye na gargajiya
Modi na duba sojoji masu fareti a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja

Asalin hoton, X/Narendra Modi

Bayanan hoto, Shugaba Modi ya samu karramawar faretin sojoji a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja.
Firaiministan Indiya, Narendra Modi da shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu

Asalin hoton, X/Bola Tinubu

Bayanan hoto, A lokacin ziyarar shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karrama Modi da lambar yabo ta GCON.
Firaiministan Indiya, Narendra Modi da shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Asalin hoton, X/Bola Tinubu

Bayanan hoto, Shugabannin Najeriya da na Indiya sun amince su kara bunkasa kawance a tsakaninsu a fannin tsaron teku da bayanan sirri da kuma yaki da ta’addanci.