Southampton ta kori kocinta bayan rashin nasara a hannun Tottenham

Asalin hoton, PA Media
Ƙungiyar Southampton mai buga gasar Premier ta Ingila ta kori kocinta Russell Martin bayan Tottenham ta lallasa ta da ci 5-0 ranar Lahadi.
Martin mai shekara 38 ya taimaka wa Southampton komawa gasar Premier a shekarar da ta gabata a kakar wasansa ta farko, inda ya doke Leeds United a wasan neman gurbi a filin wasa na Wembley.
Sai dai rashin nasara a hannun Tottenham ita ce karo na 13 da Southampton ta yi a kakar wasa ta bana bayan buga wasa 16.
Nasara ɗaya tilo da suka yi ita ce a karawa da Everton a watan Nuwamba, sai kuma ƙwallo 11 da suka zira a raga - wadda ita ce mafi ƙaranci a bana.
"Tun daga farkon kaka, mun san irin ƙalubalen da za mu shiga a shekarar nan musamman wajen buga wasa a gasa mafi wahala a duniya," a cewar wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar.
"Sai dai kuma, abin da muke gani ƙarara yake. Mahukunta sun goyi bayan Russel da abokan aikinsa, kuma mun yi ta bayyana fatanmu a fili.
"Muna yin amfani da wannan damar wajen gode wa Russel da abokan aikinsa saboda jaijrcewar da suka nuna cikin wata 18 da suka wuce."
Kocin ƙungiyar na 'yan ƙasa da shekara 21, Simon Rusk, shi ne zai karɓi aikin riƙon ƙwarya, kuma wasansa na farko da Liverpool ne a gasar Carabao CUp ranar Laraba.











