An hukunta Mourinho saboda jan hancin kociyan Galatasaray

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da Jose Mourinho daga jan ragama wasa uku, saboda samunsa da laifin jan hancin kociyan Galatasaray, Okan Buruk, bayan tashi daga Turkish Cup.
Lamarin ya fatu ne ranar Laraba, bayan tashi daga karawar da aka yi a filin Sukru Saracoglu, inda Galatasaray ta yi nasarar doke Fernerbahce 2-1.
Mourinho ya je ya ja hancin Buruk, lokacin da yake tafiya, wanda nan take ya fadi kasa ya kuma rufe hancinsa da tafin hannunsa biyu.
Haka kuma an ci tarar tsohon kociyan, Chelsea da Manchester United da kuma Tottenham, Lira 292,500, wato kimanin (£5,955).
Shi kuwa mataimakin Mourinho, Salvatore, an dakatar da shi wasa huɗu, saboda cin zarafi da zagin ƴan wasan Galatasaray.
An kuma bai wa ɗan wasan Fenerbahce, Mert Yandas da na Galatasaray, Kerem Demirbay da Baris Yilmaz jan kati, saboda hannu da suke da shi a hatsaniyar.
Daga baya an hukunta Yandas mai shekara 30 da cewar zai yi hutun wasa ɗaya.
Tun dama dangan taka ta yi tsami tsakanin Galatasaray da Fernerbahce a watan Fabrairu, inda Galatasaray ta ce za ta ɗauki matakin shari'a kan Mourinho da cewar ya yi kalaman wariyar launin fata.
Ranar Juma'a Fernerbahce ta sanar cewar masu shigar da kara na Turkiya sun kori karar da Galatasaray ta shigar kan Mourinho.











