Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Katin shaidar zama a sansanin gudun hijira da karena kawai na tsira da su'
Cikin wani dare dakarun Isra'ila suka shiga sansanin ƴan gudun hijira na Jenin a Gabar Yamma da Kogin Jordan inda suka umarci Falasɗinawa 20,000 su bar muhallansu, Jumaa Zawayda mai shekaru 66 ya ce ba zai amince ba.
''Duk iyalaina sun fice, na shaida musu cewar zan zauna, idan dakarun Isra'ila sun kawo wa gidanmu mamaya zan hana su ruguza mana shi.''
Abinda ya biyo baya, shi ne kwanaki uku cikin fargaba tare da jiyo ƙarar harbin bindiga ba ƙaƙƙautawa, fashewa da jirage marasa matuƙa ne suke sintiri a unguwarmu da kuma bayar da umarnin da Jumaa ya ce ba zai yiwa biyayya ba.
Daga nan sai aka ɗauke wutar lantarki da ruwa, bayan batirin wayarsa ya rasa caji ne Jumaa ya ce ba zai iya ci gaba da zama ba.
A yanzu watanni uku bayan faruwan lamarin, Jumaa na tsaye kan tudun birnin Jenin inda yake kallon yadda birnin sansanin ƴangudun hijira ya zama kufai yayin da sojojin Isra'ila suka hana mutane komawa.
Yana ƙoƙarin gane ko gidansa na daga cikin waɗanda sojojin Isra'ila suka lalata yayin da suka kai wa ƙungiyoyin mayaƙan Falasɗinawa hari a sansanin. Ana jiyo sautin fashewa daga ƙasa.
Jumaa cikin yanayin juyayai ya bayyana cewar ''wasu mutane sun shaida masa cewar akwai yiwuwar an rushe gidansa."
Magidancin mai ƴaƴa tara, a baya yana aiki da kamfanin gine-gine, ya zauna tsawon wata uku a wata makaranta da aka mayar matsugunin waɗanda suka rasa muhallansu.
A yanzu ya koma zama a gidan ɗaliban jami'a tare da ƴan'uwansa.
Kafin ɓarkewar yaƙin a Gaza a watan Oktoban shekara ta 2023, Isra'ial na fafatawa da ƙungiyoyin mayaƙa a gaɓar yamma da kogin Jordan.
Wasu ƙungiyoyi sun ɓulla a sansanin ƴangudun hijirar da aka ƙirƙira saboda Falasɗinawan da suka tsere ko wadanda aka kora daga gidajensu ya yin yaƙin da ya biyo bayan samar da ƙasar Isra'ila a shekara ta1948.
Manyan ƙungiyoyin a sansanin ƴan gudun hijira na Jenin na alaƙa da Hamas.
Mayakansu sun kai wa sojin Israila hare-hare a wasu lokutan kuma su na kaiwa Yƴan Isra'ila da ke zaune a gaɓar yamma da kogin Jordan.
Yan Jarida sun yi kiyasin yawan mayaƙan ya kai 150 a sansanin Jenin da kewaye kafin farmakin baya-bayan nana da Isra'ila da kuma Hukumar Falasdin suka kai.
Hukumar Falasdin wadda ke shugabancin yankunan gabar yamma da kogin Jordan ta kaddamar da farmaki a sansanin na Jenin a watan Disamban bara, dakarun ta sun janye bayan sojin Isra'ila sun fara aiki a watan Janairu.
Ministan Tsaron Isra'ila ya kira sansanin da ''sheƙar ƴan ta'adda'' a watan Janairu suka zafafa kaiwa ƙungiyoyin hare-hare a ciki ta hanyar shiga da garƙame wadansu sansanin ƴan gudun hijirar a Arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan inda ya zama matsugunin dubban Falasdinawa.
Ta bayar da mazauna umarnin ficewa sannan ta fara rusa gine-gine ya yinda ta baiwa wasu magidanta damar tattara kayan su cikin ƙanƙanin lokaci.
Amma da yadda Isra'ila ta toshe kusan dukkan hanyoyin zuwa sansanin ƴan gudun hijira kuma bata sanar da gine-ginen da ta rusa a hukumance ba, Falasdinawa da dama na cikin damuwa ko suna da gidajensu idan sun koma.
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Falasdin a Majalisar Dinkin Duniya Unrwa ta ce alkalummanta sun ce Isra'ila ta ƙona aƙalla gine-gine 260 da ke ɗauke da gidaje kusan 800 a lokacin "Operation Iron Wall", wanda ke mayar da hankali kan sansanin ƴan gudun hijira uku a Arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan: Jenin da Tulkarem da kuma Nur Shams.
Hukumar Unrwa ta ce aƙalla Falasdinawa 42,000 ne suka tsere daga sansanonin tun watan Janairu.
A watan Fabarairu, sojin Isra'ila sun sanar da kashe mayaƙa 60 sannan sun kama wasu 280. Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin ta ce an kashe mutane 100 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tun da Isra'ila ta fara yaƙi a watannJanairu zuwa wannan rana.
Ministan Tsaro Israel Katz yace sojoji suna lalata makamai da gine-gine, ya kuma ƙara da cewar ya bayar da umarnin soji su ci gaba da zama a sansanin tsawon shekara guda kuma su hana mutane komawa.
Sojojin Isra'ila sun shaiwa BBC cewar mayaƙan na amfani da yawan fararen hula wajen yin garkuwa abinda ke jefa rayuwar farar hula a hatsari sakamakon fashewar makaman da aka ɓoye.
Ranar 1 ga wayan Mayu, Isra'ila ta baiwa jami'an Falasdin a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan sabuwar taswirar gine-gine 106 da zata rusa a Tulkarem da sansanin ƴan gudun hijira na Nur Shams cikin sa'o'i 24 masu zuwa.
Amma sanarwar ta ce magidanta za su iya neman damar komawa don dauko kayansu masu muhimmanci.
Hukumomin Agaji sun ce yaƙin da Isra'ila ke yi sa Falasdinawa sun yi ƙaura mafi girma a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan cikin shekaru da dama.
Yayin da ake naɗar hira da magajin garin Jenin, BBC ta shaida yadda dakarun Isra'ila suka tsare Falasdinawa da dama da suka hada da ma'aikatan birni da ke ƙoƙarin shiga sansanin don bu'de hanyar zuwa asibiti. An tsare su tsawon sa'o'i uku kafin a sake su.
"Akwai ƙalubale wajen rabawa mutane kayan amfani. Kamar yadda kowa ya sani an rushe gine-ginen sansanin Jenin gabadaya," in ji magajin gari Mohammad Jarrar.
"Burin Isra'ila shi ne mayar da sansanin Jenin wurin da ba za a iya rayuwa a ciki ba, kuma ina shaida maka a yanzu ba za a iya zama a wurin ba."
Jumaa na daga cikin Falasdinawa da suka rasa matsugunnansu wadanda sojojin Isra'ila suka bai wa wata ƴar gajeriyar damar ziyarar gidansa don kwaso wasu kayan amfani.
Ya samu damar daukar katin shaida na Majalisar Dinkin Duniya da karensa.
Bayan watanni biyu cikin watan Maris, Isra'ila ta ba da taswirar gine-gine sama da 90 da ta gano cewa za a ruguje a Jenin.
Akwai alamar gidan Jumaa na daga ciki.
Sojojin Isra'ila sun shaida wa BBC cewar ya zama tilas a rushe wadannan gine-gine don dakarunsu su samu damar zirga-zirga, amma ba su tabbatar da cewar an rusa gidan Jumaa ba.