Napoli na son Grealish, Tottenham na sa ido kan Mainoo

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan Manchester City da Ingila Jack Grealish mai shekara 29, na cikin 'yanwasan da Napoli ke zawarci. (Corriere dello Sport - in Italian)
Javi Guerra ya yi watsi da tayin sabunta kwantiraginsa da Valencia, yayin da Manchester United ke sa ido kan ɗanwasan na tsakiya mai shekara 22 daga Sifaniya. (Marca - in Spanish)
Tottenham na bibiyar ɗanwasa Kobbie Mainoo, yayin da ɗanwasan na Manchester United bai kammala amincewa da tsawaita kwantiraginsa ba, wanda zai kare a 2027. (tbrfootball.com)
Atalanta na shirin mika tayi kan ɗanwasan Liverpool da Italiya, Federico Chiesa mai shekara 27, idan Juventus ta iya cimma yarjejeniyar biyan fam miliyan 43 kan ɗan wasan Najeriya, Ademola Lookman, mai shekara 27. (Football Italia)
West Ham na tattaunawa da Callum Wilson kan ɗanwasan Ingila mai 33 daga Newcastle. (Sky Sports)
Spurs na sa ido kan ɗanwasan Bayern Munich, Joao Palhinha. Kungiyar a shirye take a tattauna da ita kan ɗanwasan mai shekara 30 na Portugal. (Florian Plettenberg)
RB Leipzig ta sanya sunan ɗanwasan tsakiya Xavi Simons cikin 'yanwasanta da za su soma atisaye duk da cewa ana alakanta matashin mai shekara 22 da Chelsea.(Standard)
Borussia Dortmund na son cimma yarjejeniya da ɗanwasan Brighton mai shekara 20, Facundo Buonanotte. Ɗan wasan na Argentina ya karkare kakar bara a zaman aro da Leicester City. (Sky Sports)
Tattaunawa tsakanin Marseille da Feyenoord ta yi nisa kan ɗanwasan Brazil, Igor Paixao.(RMC - in French)
Leeds United na da fatan ganin ta cimma yarjejeniya da ɗanwasan mai shekara 25. (Yorkshire Evening Post)
Ɗanwasan tsakiya a Turkiyya Hakan Calhanoglu ana cewa yana yunkurin barin Inter Milan amma ɗanwasan mai shekara 31 na son zama a Italiya. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester City na son ci gaba da zama da Ederson duk da kwaɗayin da Galatasaray ta nuna kan mai tsaron raga ɗan shekara 31 daga Brazil. (The Independent)
Fulham na da yaƙinin ci gaba da zama da ɗanwasanta na tsakiya Seth Ridgeon duk da zawarcin Manchester United da Liverpool da Chelsea kan matashin mai shekara 16 daga Ingila.(Standard)










