An dakatar da Nunez daga buga wa Uruguay wasa biyar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An dakatar da ɗan ƙwallon Liverpool, Darwin Nunez daga buga wa Uruguay wasa biyar, bayan faɗa da ya yi da magoya bayan Colombia.

Lamarin ya faru ne a Copa America a bana a Amurka a karawar da Colombia ta yi nasara ta kuma kai zagayen karshe.

Nunez, mai shekara 25 ya je ya yi faɗa da magoya bayan Colombia a wajen zamansu, bayan da aka busa tashi a karawar daf da karshe a watan Yuli.

An kuma ci tarar ɗan wasan £15,145.

Ranar Laraba, hukumar ƙwallon kafa ta Kudancin Amurka ta sanar da hukuncin da ta dauka a kan Nunez da wasu da ta samu da laifi.

Shi kuwa ɗan wasan Tottenham, Rodrigo Bentancur, mai shekara 27, an dakatar da shi wasa huɗu.

Ɗan wasan Napoli, Mathias Olivera da na Barcelona, Ronald Araujo da na Atletico Madrid, Jose Maria Gimenez, an dakatar da kowanne wasa uku.

Argentina ce ta lashe Copa America, bayan da ta yi nasara a kan Colombia.