Man United ta yi waje da Arsenal a FA Cup na bana

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta yi ban kwana da FA Cup na bana, bayan da Manchester United ta yi waje da ita a bugun fenariti da cin 5-3 a Emirates ranar Lahadi.

Manchester United ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Bruno Fernandez, bayan da suka koma zagaye na biyu.

An bai wa Diego Dalot jan kati, sakamakon keta da ya yi wa Mikel Merino, wanda tun farko yana da katin gargaɗi.

Daga baya ne Gunners ta farke ƙwallon ta hannun Gebriel, hakan ya sa wasan na hamayya ya koma 1-1.

Bayan da karawar ta nutsa, Arsenal ta samu bugun fenariti, sakamakon da Harry Maguire ya ɗan taɓa Kai Havertz da hannu a cikin da'ira ta 18.

Ƙyaftin ɗin Arsenal, Martin Odegaard ne ya buga fenaritin, sai dai mai tsaron ragar United, Altay Bayindir ya tare ƙwallon.

Haka suka buga minti 90 suka tashi ba ci, daga nan aka kara musu minti 30, nan ma ba a samu gwani ba.

Daga nan aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda United mai rike da kofin ta kai zagayen gaba.

Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier League, bayan wasannin mako na 20, ita kuwa United tana ta 13 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

Wasa bakwai da ke gaban Arsenal nan gaba:

Premier League Asabar 25 ga watan Janairu

  • Wolves da Arsenal

Champions League Laraba 29 ga wwatan Janairu

  • Girona da Arsenal

Premier League Lahadi 2 ga watan Fabrairu

  • Arsenal da Man City

League Cup Laraba 5 ga watan Fabrairu

  • Newcastle da Arsenal

Premier League Asabar 15 ga watan Fabrairu

  • Leicester da Arsenal

Premier League Asabar 22 ga watan Fabrairu

  • Arsenal da West Ham

Premier League Talata 25 ga watan Fabrairu

  • Nottm Forest da Arsenal