Garnacho da Mainoo ba za su buga wa kasashensu wasa ba a Oktoba

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Alejandro Garnacho da Kobbie Mainoo da Noussair Mazraoui ba za su buga wa tawagoginsu wasa ba a cikin watan Oktoba ba.

Kenan Garnacho ba zai yi wa Argentina wasan neman shiga gasar kofin duniya ba, Mainoo ba zai buga wa Ingila Nations League ba, shi kuwa Mazraoui ba zai yi wa Morocco wasa ba.

Tun farko an gayyaci Garnacho wasan da Argentina za ta kara da Venezuela tare da takwaransa, Lisandro Martinez.

To sai dai mai shekara 20 na fama da jinya, wanda ya sanar a kafarsa ta sada zumunta cewar ba zai buga wa Argentina karawar neman shiga gasar kofin duniya ba.

Shi dai Alejandro ya fara yiwa Argentina tamaula a bara, wanda kawo yanzu ya yi mata karawa bakwai.

Shi kuwa Mainoo da kyar ne idan zai buga Ingila Nations League da za ta kara da Girka da kuma Finland, sakamakon jinya.

Matashin ya yiwa Ingila karawa 13 tun daga lokacin da ya fara yi mata tamaula a cikin watan Maris.

Mazraoui ya ji rauni a wasan da aka tashi 0-0 tsakanin Aston Villa da Manchester United a Premier League ranar Lahadi, kenan ba zai yiwa Morocco wasan neman shiga gasar kofin Afirka ba.