Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real ta rage tazarar maki tsakani da Barca ya koma saura huɗu
Real Madrid ta je ta yi nasara a kan Getafe da cin 1-0 a wasan mako na 33 a La Liga da suka fafata ranar Laraba.
Real ta ci ƙwallon ta hannun Arda Guler tun a minti na 21 da take leda, hakan suka tashi a karawar da ta kai ƙungiyar Santiago Bernabeu ta haɗa maki ukun da take bukata.
Real Madrid wadda take ta biyun teburi mai maki 72, ta rage tazararta da Barcelona mai jan ragama zuwa maki huɗu,
Da yake Real za ta buga wasan karshe a Copa del Rey da Barca ranar Asabar da Barcelona, hakan ya sa ba ta fara wasan Getafe da wasu fitattun ƴan ƙwallonta ba.
Kimanin ƴan wasa shida Real Madrid ta canja daga waɗan da suka doke Athletic Bilbao 1-0 a gasar La Liga ranar Lahadi.
Waɗan da ta ajiye a benci sun haɗa da Antonio Rudiger da Jude Bellingham da Eduardo Camavinga da Luka Modric da Dani Ceballos da kuma Rodrygo.
Hakan ya sa ta maye gurbinsu da Lucas Vazquez da David Alaba da Fran Garcia da Arda Guler da Brahim Diaz da kuma Endrick.
Kylian Mbappe bai buga karawar ba, sakamakon raunin da ya ji a wasan da Arsenal ta ci Real Madrid 2-1 a Champions League a kwata fainal a Santiago Bernabeu.
Ƴan wasan Real Madrid 11:
Courtois, Vasquez, Asencio, Alaba, Garcia, Tchouameni, Valverde, Guler, Brahim, Endrick, Vini Jr.
Masu jiran ko-ta-kwana:
Lunin, Gonzalez, Bellingham, Modric, Rodrygo, Vallejo, Ceballos, Rudiger, Gonzalo.