Arsenal ta je ta lallasa Sporting a Champions League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sporting Lisbon ta yi rashin nasara 5-1 a hannun Arsenal a Champions League ranar Talata a karawa ta biyar-biyar.

Arsenal ta ci ƙwallayen ta hannun Gabriel Martinelli da Kai Havertz da Gabriel Magalhães da Bukayo Saka da kuma Leandro Trossard.

Mai masaukin baƙi, Sporting wadda kocinta, Ruben Amorim ya bar kungiyar zuwa Manchester United a bana, ta zare ɗaya ta hannun Gonçalo Inacio.

Da wannan sakamakon Arsenal ta yi sama zuwa mataki na bakwai da maki 10, bayan cin wasa uku da canjaras ɗaya aka doke ta karawa ɗaya.

Ita kuwa Sporting mai maki 10 ta yi kasa zuwa mataki na takwas, bayan nasara uku da canjaras ɗaya da rashin nasara ɗaya.

Wannan shi ne karo na bakwai da suka kece raini a tsakaninsu a gasar ta zakarun Turai, inda Arsenal ta yi nasara karo na uku da canjaras huɗu.

Ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba Arsenal za ta je West Ham a Premier League, sannan ta karɓi bakuncin Mancheste United ranar 4 ga watan Disamba a babbar gasar tamaula ta Ingila.