Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Raya ne gwarzon Arsenal na watan Satumba
David Raya ne ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Arsenal na watan Satumba, wanda magoya bayan ƙungiyar suka zaɓa.
Wanda ya lashe safar zinare a matakin wanda ƙwallaye da yawa bai shiga ragarsa ba da a bara, karon farko da ya zama gwarzon Gunners na wata.
A labarin da Arsenal ta wallafa a shafinta na Intanet, Raya ya doke wadanda suka yi takara da ya haɗa da Gabriel da Bukayo Saka da William Saliba ka kuri'a kaso 44 cikin 100.
Ya buga wasan Tottenham ƙwallo bai shiga ragarsa ba da taka rawar gani a Atlanta da tare penaritin Mateo Retegui, inda Gunners ta samu maki a Italiya.
Haka kuma ya taka rawar gani a wasan da Arsenal ta je ta tashi 2-2 a Etihad da Manchester City da doke Leicester City 4-2 a Premier League.
Raya shi ne mai tsaron raga na farko da ya lashe ƙyautar gwarzon Arsenal na wata-wata tun bayan Aaron Ramsdale a Nuwambar 2021.
Wasa ukun da ke gaban Arsenal:
Premier Asabar 19 ga watan Oktoba
- Bournemouth da Arsenal
Champions League Talata 22 ga watan Oktoba
- Arsenal da Shakhtar
Premier Lahadi 27 ga watan Oktoba
- Arsenal da Liverpool