Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd za ta sanya Rashford a kasuwa, Arsenal na nazari kan Vlahovic
Manchester United za ta iya sayar da ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford mai shekara 27 a kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Junairu. (Sky Sport Germany)
United ta sanya Rashford a kasuwa a bazarar da ta gabata kuma a halin yanzu za ta saurari tayin da za ayi ma ta a kan ɗan wasan. (Telegraph)
Arsenal ta na nazarin miƙa tayi kan ɗan wasan gaban Juventus da Serbia Dusan Vlahovic mai shekara 24 a watan Junairu.(TeamTalk)
Ɗan wasan baya na Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 33 na da niyyar rattaba hannu kan sabon kwantiragi da Liverpool duk da cewa ya yi watsi da tayin farko da kulob ɗin ya yi masa. (Football Insider)
Barcelona ta iya yi wa Dani Olmo rajista don buga gasar La liga zuwa ƙarshen watan Disambane kaɗai, amma ɗan wasan na iya kasancewa mai zaman kansa idan har ba ta sake yi masa rajista ba a watan Junairu. (Mundo Deportivo)
Arsenal na sha'awar ɗaukar Dan Ashworth a matsayin sabon darektan wasanninta bayan ya raba gari da Manchester United. (ESPN)
AC Milan za ta iya barin kyaftin ɗinta Theo Hernandez ya bar kulob ɗin amma za ta bukaci tayin da bai yi ƙasa da fam miliyan 41 ba kan ɗan wasan faransan mai shekara 27. (Calciomercato)
Chelsea ba za ta amince ɗan wasan bayanta Tosin Adarabioyo ya tafi a matsayin aro ba a watan Junairu, yayin da aka rawaito cewa West Ham na zawarcin ɗan wasan mai shekara 27. (Football Insider)
Ana sa ran ɗan wasan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 32, zai bar Manchester United a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Fabrizio Romano)
Ana samun ci gaba a tattaunawar da Liverpool ke yi kan sabuwar yarjejeniya da ɗan wasan gaban Masar, Mohamed Salah, mai shekara 32. (Sky Sports)
Newcastle United na zawarcin ɗan wasan PSV Eindhoven ɗan ƙasar Belgium Johan Bakayoko, mai shekara 21, gabannin buɗe kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu. (Telegraph)