Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa wasu ƙasashe suka daina bai wa hukumar kula da ƴan gudun hijrar Falasɗinawa tallafi?
Yayin da ƙasashen yammacin duniya suka dakatar da bayar da tallafi ga Hukumar kula da ƴan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, bayan zargin da Isra'ila ta yi na cewa wasu tsirarun ma'aikatanta suna da hannu a harin da Hamas ta kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, mun duba abin da UNRWA ke yi da kuma yadda ake samar mata kuɗi.
Mece ce UNRWA?
UNRWA tana nufin Hukumar bayar da agaji da ayyuka ta Majalisar Ɗinkin Duniya domin ƴan gudun hijirar Falasɗinawa a Gabas ta Tsakiya.
Tana gudanar da makarantu da ayyukan jin ƙai da cibiyoyin kiwon lafiya tare da rarraba kayan abinci ga Falasɗinawa ɗan gudun hijira miliyan 5.9 a Gaza, da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ciki har da Gabashin Kudus, da Lebanon da Siriya da Jordan.
Yaushe aka kafa ta?
An kafa hukumar ne a shekara ta 1949 domin taimaka wa ƴan gudun hijirar Falasɗinawa bayan kafa ƙasar Isra'ila da yaƙin 1948.
Kimanin Falasɗinawa 750,000 ne suka yi gudun hijira ko kuma aka tilasta musu barin ƙasarsu a wani abin da suka kira Nakba ko kuma “Bala’i”.
Hukumar ta ce ta bayar da gudummawa ga "jin daɗi da ci gaban ƴan gudun hijirar Falasdinawa".
Ta yaya ake samar wa hukumar kuɗi?
Galibi gudumawar sa-kai ne da kuɗaɗe daga ƙasashen duniya masu bayar da tallafi.
Babbar mai bayar da gudumawa ita ce Amurka, wadda ta bayar da gudummawar dala miliyan 343.9 a shekarar 2022, yayin da Jamus ta kasance ta biyu mafi girma, ta bayar da gudumawar dala miliyan 202.
Idan aka haɗa, waɗannan ƙasashe biyu sun ƙunshi kusan rabin kuɗin da UNRWA ta samu na dala biliyan 1.17.
Me yasa manyan masu ba da tallafi na Yamma suka dakatar da tallafinsu?
Sama da ƙasashe 10 da suka haɗa da Amurka da Jamus sun dakatar da bayar da kuɗaɗe ga hukumar sakamakon zargin da hukumar tattara bayanan sirrin Isra'ila ta yi na cewa aƙalla mambobin UNRWA 12 na da hannu a harin da Hamas ta kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda aka kashe fiye da Isra'ila 1,200 tare da garkuwa da wasu fiye da 240 zuwa zirin Gaza.
Me Majalisar Dinkin Duniya ta ce?
A ranar Asabar da ta gabata, shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce an kori ma’aikata tara, ɗaya ya mutu, kuma suna ƙoƙarin tantance sunayen mutane biyu na ƙarshe da Isra'ila ke zargi. Ana kuma gudanar da bincike mai zaman kansa.
Ƙasashen da suka dakatar da tallafin sun haɗa da Austria da Australia da Canada da Finland da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Netherlands da kuma Burtaniya.
Ireland da Norway da kuma Spain sun ce za su ci gaba da ba da tallafi ga hukumar.
Me hukumar UNRWA ke yi a Gaza?
Hukumar na da ma'aikata 13,000 kuma ita ce babbar hukumar Majalisar Dinkin Duniya a Gaza.
UNRWA tana gudanar da ayyukan taimako a wuraren kiwon lafiya da na ilimi, ciki har da cibiyoyin horar da malamai da makarantun firamare kusan 300, da kuma samar da litattafai da ke ilmantar da matasan Falasdinawa.
Bayan ɓarkewar yaƙi a Gaza
Galibin al'ummar Gaza miliyan 2.3 sun tsere daga kudancin yankin kuma akalla Falasdinawa miliyan ɗaya ke samun mafaka a cibiyoyin UNRWA.
Ma'aikatar lafiya ta Gaza a ƙarƙashin ƙungiyar Hamas ta ce Falasɗinawa sama da 26,000 galibi mata da ƙananan yara ne aka kashe tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama da ta ƙasa a matsayin ramuwar gayya kan harin na ranar 7 ga Oktoba.
Kafin wannan lokacin, manyan motoci 500 ne ke shiga Gaza a kowace rana, amma yanzu haka ya yi ƙasa, ya koma motoci kusan 200.
An sha samun faifan bidiyo na mutane da ke hawa kan manyan motocin agaji da ke shiga yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan biyu na buƙatar agajin abinci.
UNRWA ta kuma ce an kashe aƙalla ma'aikatanta 142 a Gaza.
Kwamishinanta Janar Philippe Lazzarini ya fitar da wata sanarwa da kakkausar murya kan rage samar da kuɗaɗen.
"Falasɗinawa a Gaza ba sa buƙatar wannan karin hukunci na gama-gari," in ji shi. "Wannan ya ɓata mana duka."
Me Isra'ila ta ce?
Ya zuwa yanzu dai BBC ba ta ga bayanan asirin da Isra'ila ta tattara ba.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun nuna cewa wata ƙila an yi amfani da motoci da kayan aiki na UNRWA wajen kai harin na ranar 7 ga Oktoba.
Wani mashawarcin firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, Mark Regev, ya shaida wa BBC a ranar Juma'a cewa harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba ya haɗa da "mutanen da UNRWA ke biyan su albashi."
Mista Regev ya kuma yi magana kan wata ƴar Isra’ila da aka yi garkuwa da ita, wadda a lokacin da aka sake ta, ta ce an tsare ta a gidan wani da ke aiki da UNRWA.