Sporting ta fitar da Arsenal a Europa League

An wallafa

Arsenal ta yi ban kwana da Europa League na bana, bayan da Sporting ta fitar da ita a bugun fenariri a Emirates ranar Alhamis.

Tun farko sun tashi 1-1, inda Granit Xhaka ya ci kwallon a minti na 19, kuma na biyar da ya zura a raga a kakar nan a dukkan fafatawar da ya yi wa Arsenal.

Sporting ta farke ta hannun Pedro Goncalves, bayan da suka koma zagaye na biyu a fafatawar.

Gabriel Martinelli ya buga ta sa fenaritin amma golan Sporting, Adan ya tare kwallon da haka kungiyar Portugal ta kai zagayen baga da cin 5-3.

Sporting ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Pedro Goncalves jan kati.

A makon jiya Gunners ta tashi 2-2 a gidan Sporting a wasan zagayen farko na kungiyoyi 16.

Kungiyoyin da suka kai quarter final:

Feyenoord daga Netherlands

Juventus daga Italiya

Leverkusen daga Jamus

Man United daga Ingila

Roma daga Italiya

Sevilla daga Sifaniya

Sporting daga Portugal

Union Saint-Gilloise daga Belgium

Arsenal tana matakin farko a teburin Premier League da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Ranar Lahadi Arsenal za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan mako na 28 a Premier League.