Ban san ina da baiwa ba sai da wasu suka hango min - Sani Maiƙafiya

Ban san ina da baiwa ba sai da wasu suka hango min - Sani Maiƙafiya
An wallafa

Mawaƙin Hausa Sani Saminu Plumber - wanda aka fi sani da Sani Maiƙafiya - ya faɗa wa BBC Hausa cewa tsautsayi ne ya sa waƙar da ya yi ta karaɗe gari.

Cikin wata hira ta musamman, mawaƙin ya ce bai san cewa yana da baiwar waƙa ba sai da wasu mawaƙa a faɗin duniya suka ga waƙarsa ta "talaka yana magana" kuma suka ce yana da baiwar.

Sani wanda har wa yau ake yi wa laƙabi da talaka, ya ce shi "almajiri" ne mai sana'ar gyaran famfo.

A sha kallo lafiya.