Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda labarin DPO da ya ƙi karban cin hancin miliyan ɗaya daga ɗan fashi ya ja hankali
Labarin wani jami'in 'yansanda na gunduma, wato DPO, da yaƙi karban cin hancin miliyan guda daga wajen wani kasurgumin ɗan fashi ya ja hankalin mutane a Najeriya.
DPOn a jihar Kaduna ya kama mutumin da ake zargin kasurgumin ɗan bindiga ne da ake ta nema ruwa a jallo. Sannan aka bankaɗo tsabar wasu kuɗi naira miliyan biyu da dubu dari uku.
Kama ɗan bindigan da jami'in 'yan sandan ya yi dai ya kai ga samar da wasu muhimman bayanan sirri ga rundunar 'yan sandan, har abin ya taimaka wajen kama wasu da ake zargi da yawan satar mutane a babban birnin tarayya Abuja.
ASP Mansir Hassan, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar ta Kaduna, ya shaida wa BBC cewa kwamishinan 'yan sandan Kaduna CP Audu Ali ya jinjina wa jami'in ɗan sandan
"Tun daga rana ta farko da wannan alamari ya faru, kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna CP Audi Ali ya gayyaci wannan DPOn kuma an jijina mi shi, akwai kyauta da ake badawa ta DPOn mafi kwazo na karshen wata da aka ba shi".
ASP Mansir Hassan ya ce an mika sunan DPOn ga hedikwatar rundunar 'yan sanda ta kasa a jerin sunayen wadanda suka aikata abin a zo gani.
Ya kuma ce ɗan sanda ya yi nasarar cafke wani mashahurin ɗan fashi wanda sakamakon kama shi da aka yi ‘yansanda sun daƙile wani hari da 'yan bindiga su ka so su kai a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
"Har illa yau shi wannan DPOn ya nuna bajinta wajen kama wani mashahurin ɗan fashi wanda sakamakon kama shi muka samu bayyanan sirri inda a baya-baya nan mun kama 'yan fashi 8 a yayin da suke kokarin aiwatar da mumunan ta'adi a hanyar kaduna zuwa Abuja.
"Mun samu nasarar kamasu tare da makamai da kuɗi kuma nan bada jimawa ba za a gurfana da su a gaban kotu".
Rundunar 'yan sanda ta kuma ce jami'anta sun yi nasarar kama wani da ake zargi da safarar makamai wanda aka same shi da harsasai kusan dari biyu