Na yi farin cikin lashe kofin farko a rayuwata - Harry Kane

Harry Kane

Asalin hoton, @FCBayernEN

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Harry Kane ya ce ya yi farin cikin kawo ƙarshen fatarar kofi a rayuwarsa ta tamaula bayan lashe kofin Bundesliga a Bayern Munich.

A ranar Lahadi ne Bayern ta lashe kofin Bundesliga bayan Bayer Leverkusen ta tashi wasa 2-2 da Freiburg.

Kaftin ɗin na Ingila ya kafa sabon tarihin inda ya zura ƙwallo 60 a raga a wasa 60 da ya buga wa Bayern a Bundesliga, kuma zai zama na farko da ya kafa tarihin wanda ya fi yawan cin ƙwallaye a kaka biyu a jere.

"Dare ne mai muhimmanci, mun yi farin ciki tare da sauran ƴanwasa, lokaci ne da na daɗe ina jira. Na jajirce da sadaukar da kai, akwai daɗi lashe kofi kuma na farko a rayuwata," in ji Kane.

Harry Kane ya sha jin ƙamshin kofi a wasannin ƙarshe da yake a tarihin rayuwarsa ta tamaula amma sai ya ƙare ba kofin.

Ya je wasan ƙarshe a gasar cin kofin Turai ta Euro 2020 da Euro 2024 a Ingila da kuma wasan ƙarshe a gasar cin zakarun Turai a Tottenham.

Shekaru 14 kenan Harry Kane yana yunwar kofi, tun da ya fara taka leda matakin ƙwararru inda ya ci ƙwallo 447 a haskawa 694 a matakin ƙungiya da kuma ƙasarsa.