Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United ta naɗa Amorim a matsayin sabon kocinta
Manchester United ta tabbatar da naɗa Ruben Amorim a matsayin sabon kocin ƙungiyar.
Kocin mai shekara 39, wanda ɗan ƙasar Portugal ne, zai fara ne aiki ne daga ranar 11 ga Nuwamban 2024, bayan ya sanya hannu a kwantiragin aiki zuwa shekarar 2027.
Yanzu dai tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Ruud van Nistelrooy ne ke kocin riƙon ƙwarya, kuma zai ci gaba da riƙon har zuwa lokacin da Amorim zai fara aiki.
Amorim ne koci na shida da zai horar da ƙungiyar tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya, bayan shekara 26 yana horar da ƴan wasan ƙungiyar. Sannan akwai wasu guda huɗu da suka yi riƙon ƙwarya.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce, "Ruben na cikin zaƙaƙuran masu horar da ƴanwasa da suke ganiya a turai a yanzu."
Wasan farko da Amorim zai fara a ƙungiyar shi ne wasan Manchester United da ƙungiyar Ipswich a ranar 24 ga Nuwamba, sannan a ranar 28 ga Nuwamba zai jagoranci ƙungiyar domin fafatawa da Bodo/Glimt a gasar Europa.
A ranar 28 ga Oktoba ce ƙungiyar ta kori tsohon kocinta, Erik ten Hag daga aiki bayan ya yi shekara biyu a ƙungiyar.
Sai dai tun bayan da ya fara aiki ne sakamakon wasannin ƙungiyar ke kwan-gaba-kwan-baya, har ta kai ga sun raba-gari.
Erik ten Hag ya lashe kofuna biyu a shekara biyu a ƙungiyar, daga ciki akwai doke Manchester City da Man U ta yi da ci biyu da ɗaya a wasan ƙarshe na kofin FA, wanda shi ne kofin farko da ƙungiyar ta lashe bayan shekara shida.
Wane ne Amorim?
An haifa Rúben Filipe Marques Amorim ne a ranar 27 ga Janairun 1985, a birnin Lisbon da ke ƙasar Portugal. Ƙungiyar Sporting CP ta Portugal ce ta ƙarshe da ya horar kafin Manchester United.
Tsohon ɗan wasan tsakiya ne, inda ya taka leda a ƙungiyoyin Belenenses da Benfica, sannan ya buga wa Portugal wasa sau 14.
A shekarar 2017 ya yi ritaya daga taka leda, sannan ya fara aikin horar da ƴanwasa a ƙungiyar Casa Pia a shekarar 2018, amma ya ajiye aiki ba da daɗewa ba.
Daga baya ya koma ƙungiyar Braga B, kafin daga baya suka kamar da shi babbar ƙungiyar a shekarar 2019, inda ya lashe kofin Taca da Lifa a shekarar 2020.
A watan Maris na 2020 ne ya zama kocin Sporting CP, inda zuwa yanzu ya lashe kofin Taça da Liga biyu da gasar Primeira Liga bayan shekara 19 ƙungiyar ba ta lashe kofi ba, sannan ya sake lashe kogin gasar Primeira Liga a kakar 2023–24.
Ya taɓa aikin sanin makamar aiki a a ƙungiyar Manchester United a ƙarƙashin Jose Mourinho na wasu ƴan kwanaki.