Kepa Arrizabalaga na daf da zuwa aro Real Madrid

An wallafa

Golan Chelsea, Kepa Arrizabalaga na daf da komawa Real Madrid, domin buga mata wasanni aro.

Mai tsaron ragar Real Madrid, Thibaut Courtois, mai shekara 31, ya ji rauni a gwiwar kafarsa, wanda zai yi jinya mai tsawo a kakar nan.

An alakanta tsohon golan Manchester United, David de Gea, wanda bai da kungiya a yanzu haka, amma Real ta zabi daukar aron Kepa, mai shekara 28.

Kepa zai fuskanci kalubale a Chelsea a wajen Robert Sanchez, wanda aka dauko daga Brighton kan fam miliyan 25.

Kepa ya koma Chelsea daga Athletic Bilbao kan fam miliyan 71 a watan Agustan 2018 - kudi mafi tsada da aka sayi mai tsaron raga a tarihi.

Daga baya ya rasa gurbinsa a Chelsea, inda Edourd Mendy ke gabansa a sa kwazo, daga baya golan tawagar Senegal ya ji rauni.

Chelsea ta sayar da Mendy a bana ga Al Ahli mai buga gasar Saudi Arabia a cikin watan Yuni.

Kepa, wanda ya yi wa Chelsea wasa 163, an yi ta alakanta shi da komawa Bayern Munich, bayan da golanta, Manuel Neuer ya ji rauni a bara.