Wane zaɓi ne ya rage wa ɗaliban ƙasashen waje bayan haramta musu bizar Amurka?

    • Marubuci, Rebecca Thorn
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ɗalibai a sassan duniya sun ce suna cikin tashin hankali da halin rashin tabbas yayin da gwamnatin Trump ta fara shirin dakatar da bayar da takardar shiga ƙasar ga ɗaliban ƙasashen waje masu son yin karatu a Amurka, na wucin gadi.

Wata sanarwar cikin gida da kafar CBS mai alaƙa da BBC ta gani ta bayar da umarnin dakatar da bayar da bizar na wucin gadi ga ɗaliban ƙasashen waje, yayin da ma'aikatar harkokin waje ta Amurkan ta ƙara ƙaimi wajen tantance masu neman biza ta hanyar binciken shafukansu sada zumuntar masu son shiga ƙasar.

Matakin yana cikin ƙoƙarin shugaba Donald Trump na rage ƙarfin wasu jami'oin Amurka masu sassaucin ra'ayi.

Ya kuma ɗauki matakin hana jami'ar Harvard bayar da gurbin karatu ga ɗalibai ƴan ƙasashen waje, inda ya zarge ta da gaza ɗaukar mataki a kan masu tsattsauran ra'ayin ƙiyayyar Yahudawa.

Jmai'ar Harvard ta shigar da ƙara, kuma wani alƙali ya bayar da umarnin dakatar da shirin na shugaba Trump.

Waɗanne ɗalibai matakin zai fi shafa?

Ƙungiyar Open Doors mai tattara bayanan ɗaluban ƙasashen waje masu karatu a Amurka, ya ce ɗalubai miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya ne suka shiga makarantun Amurkan, daga ƙasashe 210, a zangon karatu na 2023-24,

A shekarar da ta gabata ɗaluban India ne suka na kowacce ƙasa yawa a Amurka, kuma Open Doors ta ce ɗaluban ƙasar fiye da dubu 330 ne ta tattara bayanan su a ƙididdigar da ta gudanar.

China ce ƙasa ta biyu da ta fi yawan ɗalubai a Amurka da ɗalubai dubu 280. Sai kuma ƙasashen Koriya ta kudu da Canada da Taiwan da Vietnam da Najeriya da Bangladesh da Brazil da kuma Nepal da ke biye da ita a jere.

Sai dai a ranar Laraba, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce gwamnatin Trump za ta ''soke bisar da ta bai wa ɗaluban China, cikin su kuma harda masu alaƙa da jam'yyar kwamunasanci da kuma masu karatu a fannoni masu muhimmanci sosai.''

Daga cikin tsarin akwai kuma tanadin ''ƙara tsauri kan matakan tantance yadda ake bayar da bisa'' ga jama'ar China da kuna Hong Kong.

Babu tabbacin ko ɗaluban China nawa da ke karatu a Amurka wannan mataki zai shafa.

China ta ce za ta yi ''turjiya sosai'' kan wannan mataki, tare da kira ga Amurka ta ɗauki wasu matakan na daban da za su inganta alaƙar ƙasashen.

Tuni dai gwamnatin Trump ta fara shirin mayar da wasu ɗalubai ƙasashen su, tare da soke bisar wasu dubbai.

Mr Rubio ya ce a ƙarshen watan Maris Amurka ta soke bisar ɗalubai aƙalla 300 a cikin shirin gwamnatin Trump na daƙile masu zanga-zangar goyon bayan Falaɗinawa a harabar jamia. Bai dai bayyana ko ɗaluban wace ƙasa wannan mataki zai shafa ba.

A ranar Laraba jami'ar Harvard ta shaidawa kotu cewa haramta mata bayar da gurbin karatu ga ɗaluban ƙasashen zai cutar da jami'ar sosai.

Jami'ar da ke kula da ɗaluban ƙasashen waje a jami'ar Harvard, Maureen Martin, ta ce matakin ya riga ya jefa ɗalubai da malamai cikin damuwa.

Ta ce ɗalubai suna ƙauracewa bikin yaye ɗalubai da soke tafiye-tafiyen ƙasashen waje da kuma neman komawa karatu a wasu jami'oi na daban.

Wasu sun bayyana tsoron cewa za a iya fatattakar su zuwa ƙasashen su, wajen da suke fuskantar rikici da bita da ƙullin siyasa.

Farfesa William Brustein, ƙwararre a fannin koyar da ɗaluban ƙasashen waje a jami'ar Virginia da kuma ta Pittsburg, ya ce ita ma Amurka za ta fuskanci matsala saboda wannan mataki.

"Harvard za ta iya neman hanyar ficewa daga wannan yanayi duk da cewa za a sha wahala. Amma abin damuwar shi ne sauran jami'oin gwamnati da suka dogara ga ɗaluban ƙasashen waje domin samun kuɗin shiga.''

"Za kuma mu rasa damar koyon zamantakewa tsakanin mutane daga sassan duniya a jami'ar tamu.'' in ji farfesa Brustein.

Wane zaɓi ake da shi?

Canada da Birtaniya da kuma Australia suna da ɗaluban ƙasashen waje da dama a shekarun baya bayan nan.

Sai dai an samu raguwar ɗaluban saboda sauye-sauyen da aka samu a dokokin dokokin shige da fice a ƙasashen.

A misali, Canada ta fara shirin rage yawan ɗaluban ƙasashen waje da take ɗauka, a cikin ƙoƙarin ta na rage yawan shiga ƙasar.

Birtaniya ma, inda ake da manyan jami'oi kamar Oxford da Cambridge, hukumomi suna rage yawan damar da suke bai wa ɗalubai daga ƙasashen waje.

Matakin tsuke bisar da ake bai wa ɗalubai a ƙasar ya fara aiki a watan Janairun 2924, kuma hakan na nufin ɗalubai ba za su iya zuwa tare da mata ko mazan su ba, gashi kuma an haramta wa ɗalubai sauya bisar tasu daga ta karatu zuwa ta karatu da aiki.

Australia, ɗaya daga cikin ƙasashen da ɗaluban ƙasashen waje ke yi wa yawa a duniya ta ƙayyade yawan ɗaluban da ta ke ɗauke daga waje a kowacce shekara, a cikin matakan ta na rage yawan kwararar baƙi.

Farfesa Brustein, ya ce abin da hakan zai haifar shi ne za a tilastawa ɗaluban zama a ƙasashen su, domin za a samu ƙasashe da ke ƙara zuba kuɗi don inganta ɓangaren ilimin su.

Me sauran ƙasashe ke yi?

Ga jami'oi da dama, abin da ke faruwa a Amurkan wata dama ce gare su, musamman kasancewar sun dogara ga ɗaluban ƙasashen waje domin samun kuɗaɗen shiga.

Shugaban jami'ar Hong Kong, John Lee ya ce a shirye suke su rungumi duk wani ɗalubi da ''ya fuskanci wariya daga tsarin Amurkan'' domin su ci gaba da karatun su.

"Makarantun gwamnati da masu zaman kansu za su bayar da dama ga waɗanda ke son ci gaba da karatun su a Hong Kong," in ji Lee.

Wasu makarantun Asiya ciki harda jami'ar Sunway ta Malaysia sun faɗaɗa bayar da gurbin karatun su ga ɗaluban ƙasashen waje.

"Muna da haɗin gwiwa da jami'ar Arizona ta yadda za a iya tura ɗaluban Harvard zuwa can, ko kuma wata makarantar mu.''

A nahiyar Turai, Jamus ta zamo wajen da ke jan hankalin ɗalubai daga ƙasashen waje.

An yi ƙiyasin ƙasar tana da ɗalubai fiye da dubu 400 daga ƙasashen waje.

A cikin watan Maris ɗin bana, ƙasar ta ɓullo da matakan bari ɗaluban ƙasashen waje su riƙa yin aiki na tsawon sa'oi 20 a kowanne mako, ba kamar yadda a baya aka amince su yi aikin sa'oi 10 kacal ba.

Farfesa Brustein ya ce tsarin karatu a manyan makarantun duniya ya canza sosai a cikin shekaru 15, domin haka akwai zaɓi sosai ga ɗaluban ƙasashen waje.

Ko ɗalubai na iya sauya wuraren da suke karatu zuwa wata ƙasa ta daban?

Farfesa Brustein na sa ran tsarin 'Reshen jami'a' ya yi fice sosai a yanzu.

Ya ce "Ina sane cewa jami'oin Birtaniya na da tarihin amfani da wannan tsari, kuma jami'oin Malaysian ma suna yin haka.''

Jami'ar Harvard ta wallafa jerin ƙasashen fiye da 50 a shafinta na intanet, waɗanda suke bayar da damar yin karatu a ƙasashen waje, da suka haɗa da Argentina da Ingila da Korea da Senegal da kuma Brazil.

Kawo yanzu ba ta sanar ko ɗalubai za su iya canza wuraren karatun su ba, idan aka amince da matakin na shugaba Trump.