...Daga Bakin Mai Ita tare da Murja ƙanwar Kofur Audu na shirin Daɗin Kowa
...Daga Bakin Mai Ita tare da Murja ƙanwar Kofur Audu na shirin Daɗin Kowa
An wallafa
Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Lubabatu Sani Fagge.
Daga cikin finafinan da ta shahara da su akwai Daɗin Kowa, inda ta fito a matsayin Murja - ƙanwar Kofur Audu - a fim ɗin - da kuma Lulu da Andalu.
Ta ce ta daɗe tana sha'awar shiga fim har zuwa lokacin da ta haɗi Nuhu Kansila - ɗaya daga cikin manyan taurarin Daɗin Kowa.



