Netflix: Me ke hana fina-finan Kannywood shiga manhajojin duniya?

Netflix

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ana cigaba da jiran gawon-shanun sake ganin wani fim ɗin masana'antar Kannywood da zai samu shiga manhajar kallon fina-finai na duniya, musamman Neflix, lamarin da masu ruwa da tsaki a masana'antar suka ce su kan su yana ɗaure musu kai.

A ranar 31 ga Disamban 2023 ne aka kafa tarihi a masana'antar Kannywood, inda fim ɗin 'Mati a Zazzau' ya zama na farko a cikin fina-finan Hausa da ya shiga manhajar ta Netflix, wadda manhaja ce da ake iya kallon fina-finai a ko'ina a faɗin duniya, kuma masu shirya fim suke samun maƙudan daloli, kuma ga samar da sauƙin kallo.

'Mati a Zazzau' fim ne na Rahama Sadau, wanda ta tsara domin cigaba da labarin Mati da Lado, wanda ya fara fitowa a watan Fabrairun 2020.

Tun bayan da fim ɗin na farko ya samu karɓuwa ne aka fara murnar cewa an warware ƙullin da ya daɗe yana yi wa masana'antar dabaibayi - wato rashin ingantaccen hanyoyin kasuwancin fina-finan, inda aka fara tunanin fina-finan za su fara kafaɗa da kafaɗa da takwararta ta Nollywood da ke kudancin Najeriya.

Sai dai har yanzu alamu sun nuna akwai sauran aiki ja a gaban masu shirya fina-finan, domin tun bayan fim ɗin na farko, har yanzu ba a sake karɓar wani fim ɗin ba.

Laifin waye wannan matsalar?

Ganin yadda aka daɗe ana fina-finan Hausa, da kuma ganin yadda ake da masu shirya fina-finai da ake gani ne gani na faɗa, sai wasu masu bibiyar masana'antar suke ganin laifin furudososhin da rashin kashe kuɗaɗe domin samar da fina-finai masu inganci da mahnajojin na duniya za su karɓa.

Sai dai furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya musanta wannan maganar, inda ya ce su kan su batun manhajojin na ɗaure musu kai.

A cewarsa, "To gaskiya abin da ke faruwa shi ne tun bayan da fim ɗin Mati a Zazzau ya shiga Netflix, Rahama Sadau ta zo ta zauna da mu masu shirya fina-finai da daraktoci a kan ta zama mai shiga tsakani. Har aka amince masu shirya fim za su yi haɗaka. Wasu daga cikinmu suka je Legas suka zauna da su ƴan Netflix ɗin aka yi maganganu har suka ce kowa ya kawo bayanin labarinsa, wasu ma suka gabatar musu. Daga nan kuma sai muka ji shiru."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ƙara da cewa tun bayan wannan hoɓɓasar da Rahama ta yi, har yanzu ba a sake ganin wani fim ɗin a Netflix ba.

Maishadda ya musanta zargin cewa fina-finan Kannywood ba su da inganci, inda ya ce suna da labarai masu kyau da kayan aiki.

"Akwai wani fim ɗina 'Watarana a Kano' da ya kamata a ce na kai musu, amma daga ƙarshe sai Arewa24 na kai saboda na gaji da jira kuma na ji shiru."

Ya ce a shirye suka shirya fina-finai manya, amma a cewarsa, matsalar ita ce, "ko ka shirya fim ɗin, ina za kai?"

"Ai ka ga akwai manhajar Prime Amazon, akwai fim ɗina na Aisha wanda da shi na lashe karramawar gwarzon fim ɗin da aka yi da harshen gida a bikin karrama fina-finai ta MVC 2023. Da na lashe gasar, sai suka ce za su saya, muka yi magana da su muka yi komai, suma dai abin shiru."

Ya ƙara da cewa suna da labarai, suna da ma’aikata, sannan duk wani kayan aiki da ƴan kudu suke amfani da su, suma za su iya yin amfani da su domin shirya irin fina-finan da suke yi.

"Su Netflix ɗin har yanzu babu wani ƙwaƙƙwarar abu. Ai ba kai fim ɗaya ko biyu ba ne, ya zama suna karɓar finafinan ake magana. Ka ga fim ɗin "Mai martaba' na forodusa Prince Daniel Aboki sun shiga gasar karrama fim ta duniya Oscar da shi. Ka ga wannan wani abun alhafari ne da za a gane cewa daga nan ɓangaren Kannywood muna ƙoƙari."

An samu ci gaba, amma... -Muhsin Ibrahim

Dakta Muhsin Ibrahim

Asalin hoton, FB/Muhsin Ibrahim

Dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus, ya ce lallai an samu ci gaba wajen shirya fina-finan Kannywood masu inganci.

Ya ce, "ai idan ka kalla fim ɗin "Wataran a Kano" za ka ga an samu ci gaba sosai wajen tsarawa da ɗaukar fina-finan na Hausa. Amma sai mutum ya riƙa mamakin me ya sa irin waɗannan fina-finan ba sa samun karɓuwa a manhajojin na duniya."

Sai dai Muhsin ya ce akwai gazarar ƴan Kannywood na rashin nemo hanyoyin kasuwancin fina-finan da bunƙasa su, "musamman kasancewar kasuwar tana Legas ne, ya kamata a ce yanzu sun kutsa."

Muhsin ya ƙara da cewa masu ruwa da tsaki a masana'antar suna buƙatar ƙarin hadin kai domin gano matsalolin da kuma nemo hanyoyin fuskantarsu domin magance su.

A cewar Mushin, "akwai fina-finan kudancin Najeriya da idan ka kalle su a Netflix da Amazon Prime, za ka ga ba su fi wasu daga cikin fina-finan Kannywood ba. Amma sai ka rasa me yake faruwa."

Sai dai ya ce akwai buƙatar su ƴan Netflix ɗin a Najeriya su zo su nemi fina-finan na Hausa ne da kan su.

Ya ce fina-finan kudancin suna samun kuɗi ne ta hanyar kallonsu da ake yi a manhajojin, da kuma sinima da suke da su manya na zamani a yankin, sannan ya ƙara da cewa a arewa sinama ba ta samu karɓuwar da ake buƙata ba, ballantana a samu kuɗaɗe masu yawa.

Ya ce lallai akwai buƙatar ƴan Kannywood su dage wajen tabbatar da fina-finansu suna shiga manhajojin video on demand wato VoD irin su Netflix da sauransu.