Gawarwakin da ake sa wa kankara don yiwuwar farfado da su
Gawarwakin da ake sa wa kankara don yiwuwar farfado da su
An wallafa
Yanzu akwai daruruwan gawarwaki da aka daskarar da su da kankara a fadin duniya, inda ake jira a samu ci gaban kimiyyar da zai sa a farfado da su. Sai dai wannan batu yana haifar da ce-ce-ku-ce.
Masana kimiyya na fargabar cewa hakan zai samar da rukunin wasu mutane da aka daskarar da gawarsu da kankara, wadanda a nan gaba ba za su samu tarba mai kyawu ba.



