Ɓarin da Nunez ya yi ya damu kociyan Liverpool

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Liverpool ya nuna damuwa kan halin da ɗanwasansa na gaba ya shiga bayan da ya ɓarar da damar da ƙungiyar za ta iya yin nasara a karawarta da Aston Villa inda suka yi 2-2 a gasar Premier.

Canjaras ɗin da Liverpool wadda take ta ɗaya a kan tebur ta yi a gidan Aston Villa a ranar Laraba duk da cewa ta samu maki ɗaya to amma hakan na zaman tasgaro a tazarar da take bai wa masu binta a baya a gasar musamman Arsenal.

Kociyan ƙungiyar Arne Slot ya ce yana ƙoƙarin ganin ya daidaita al'amarin ɗan wasan nasa -Nunez wanda tun bayan da ya ɓarar da kyakkyawar damar da za ta bai wa ƙungiyar nasara a karawar alamu suka nuna jikinsa ya yi sanyi.

Kociyan ya ce ba zai damu da duk wani ɓari ba musamman daga ɗan wasan da ya ci muhimman ƙwallaye biyu a karawarsu da Brentford.

'' Na fi son ya ci a wasanmu da Villa, to amma wannan abu ne na sa'a - magana ce ta dama. Babu tabbaci ɗari bisa ɗari cewa ƙwallon za ta ci.''

To amma babban abin da ya dame ni shi ne yanayinsa bayan ya ɓarar da damar, abin ya dame shi sosai ya rikita shi ya sa ya sauya daga Darwin da aka san shi.''

"Ina ganin abin ya dame shi ssaoa bayan ya ɓarar da wannan dama."

Kociyan ya ce a kullum yana son ganin ɗanwasa ya zama kamar Wataru Endo - '' a duk tsawon kaka ci gaba yake, yi ba ya waiwayen abin da ya faru a baya kuma a duk lokacin da muke buƙatarsa a shirye yake.'' In ji Slot .

A yanzu Liverpool tana ta ɗaya a teburin Premier da maki 61 bayan wasa 26, yayin da Arsenal ke bi mata da maki 53 a wasa 25, sai Nottingham Forest ta uku da maki 47 a wasa 25.