Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna sa ran Salah ya ci gaba da zama a Liverpool - Slot
Kocin Liverpool Arne Slot ya ce yana tsammanin Mohamed Salah ya ci gaba da zama a kungiyar bayan rawar da ya taka a wasan da suka tashi 3-3 da Newcastle.
Salah mai shekara 32 kwataraginsa a Anfield za ta kare a ƙarshen wannan kaka kuma a makon jiya ya ce ya ji "babu daɗi" ganin yadda ƙungiyar ta ƙi yi masa sabon ta yi.
Dan ƙasar Masar ɗin ya nuna darajar da yake da ita tana nan har gobe a wasan da suka yi da Newcastle, inda ya bai wa Curtis Jones ya ci kwallon farko a wasan, sannan daga baya ya ci biyu kafin daga bisani Fabian Schar ya farke a tashi 3-3.
Slot ya ce "a duk lokacin da muke buƙatar kwallo Mo Salah yana ci mana.
"Muna fata da sa ran zai ci gaba da wannan har zuwa wani lokaci mai tsawo. Ya ba da mamaki a zagaye na biyu, yana yi mana abubuwan ban mamaki."
Rawar ganin da Mo Salah ya yi ta cin kwallo a duka gasa
Robbie Fowler ya ci wa Liverpool kwallo 128 a Premier kuma ba shi da shakku kan yadda ƙungiyar za ta ɗauki mataki game da zaman Salah.
Da yake tattaunawa da Amazon Prime Fowler ya ce: "Bayanan Salah kan ƙoƙarinsa na cike da ban mamaki. Mun yi magana kan ci gaban kwataraginsa, eje ɗinsa zai zo domin ya sa hannu a kan yarjejeniyar a kowanne lokaci.
"Dan wasa ne da yake sauya wasa baki ɗaya. Yana da lokutan tunawa da dama. Mai nasara ne a wasanni."
Sau 37 Salah ya ke da hannu a kwallon da ya ci da kuma ya taimaka aka ci a bana, ya wuce Wayne Rooney mai 36 wanda yana cikin wadanda suka taka rawar gani a gasar a baya.
Salah ya ci kwallo a wasanni bakwai da ya buga a Premier bana, ya zama na uku da ya yi bajintar cin kwallo bakwai a wasanni a jere bayan ɗan wasan Leicester City Jamie Vardy da sabon kocinsa na yanzu Ruud van Nistelrooy.
Ya ci kwallo tare da taimakawa aka ci 325 a wasa 370 da ya buga tun bayan zuwansa Liverpool daga Roma a 2017, Steven Gerrad ne kawai yake gabansa 92 ya kuma ba da 76 aka ci a Premier.