Zaɓuka da za a yi a ƙasashe masu karfin faɗa a ji a duniya
Zaɓuka da za a yi a ƙasashe masu karfin faɗa a ji a duniya
An wallafa
A shekara ta 2024 da muka shiga, wasu manyan ƙasashe masu karfin faɗa a ji a duniya, za su gudanar da zaɓuka.
Za a yi zaɓukan ne a kusan ƙasashe 80 da suka kunshi sama da rabin mutanen duniya.
Ana sa ran wasu daga cikin zaɓukan za su ƙasance masu muhimmanci wajen sanin inda duniya ta dosa cikin shekaru masu zuwa.
Cikin manyan ƙasashen da za a yi zaɓukan akwai Amurka, Birtaniya, Rasha, Indiya da kuma Afrika ta Kudu.



