Juventus na son aron Phillips, Arsenal na nazari kan Inacio

Kalvin Phillips

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Juventus na tattaunawa da Manchester City kan aron ɗan wasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips. (ESPN)

Ɗan wasan mai shekara 28 ya gaya wa Manchester City cewa yana son barin ƙungiyar a wata mai zuwa, Newcastle United ma kuma na son aronsa. (Guardian)

Arsenal na nazari kan sayen ɗan bayan Portugal da Sporting Lisbon Goncalo Inacio mai shekara 22 a kan fam miliyan 52 a watan Janairu. (Sun)

Chelsea za ta kare duk wani yunƙuri na Tottenham na zawarcin ɗan wasanta na tsakiya na Ingila Conor Gallagher a lokacin kasuwar ƴan wasa ta Janairu duk da rashin tabbas game da kwantiraginsa a Stamford Bridge. (Football Insider)

Tosin Adarabioyo, ya gaya wa Fulham cewa yana son tafiya a bazara mai zuwa ba tare da wani kwantiragi a kansa ba. A baya Tottenham da Monaco sun nuna sha'awarsu a kan tsohon matashin ɗan bayan na Ingila. (Sun)

Tottenham za ta karkata ga wasu ƴan wasan idan ba ta ji wata ƙwaƙƙwarar magana daga ɗan bayan Faransa da Nice Jean-Clair Todibo a ƴan makonnin da ke tafe ba. Ana danganta ɗan wasan mai shekara 23 da tafiya Manchester United. (Teamtalk)

A shirye Rennes take ta raba gari da ɗan wasanta na tsakiya Nemanja Matic, a watan Janairu. A bazarar da ta wuce ne tsohon ɗan wasan na Serbia ya koma ƙungiyar ta gasar Faransa daga Roma. (L'Equipe)

Barcelona da Real Madrid na kan gaba a tsakanin ƙungiyoyin da ke son sayen Mason Greenwood, mai shekara 22, wanda a yanzu Manchester United ba ta da shirin dawo da shi Old Trafford dindindin idan ya gama zaman aro a Getafe. (Talksport)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da cewa Nottingham Forest, ta kori Steve Cooper a yanzu shi ne kan gaba a cikin waɗanda Crystal Palace ke son ɗauka kociya. Har ma ana sa ran ƙungiyar za ta tuntuɓi kocin ɗan Wales mai shekara 44 domin maye gurbin Roy Hodgson, mai shekara 76, da ke shirin sake ritaya. (Football Insider)

Matashin ɗan wasan gaba na gefe na Juventus kuma ɗan tawagar ƴan ƙasa da shekara 21 ta Ingila Samuel Iling-Junior, na ɗaukar hankalin Tottenham, da Aston Villa da kuma Brighton. (Fichajes )

Har yanzu Juventus ba ta kawar da yuwuwar sayen tsohon ɗan bayan Portugal Tiago Djalo, ba daga Lille a watan Janairu, kodayake ana ganin cinikin a bazara mai zuwa ya kasance ƙila-wa-ƙala. (Gazzetta dello Sport)

West Ham da Fulham na sha'awar matashin ɗan wasan gaba na Najeriya Akor Adams, mai shekara 23, wanda zai iya barin Montpellier a Janairu a kan kuɗin da ya kama daga fam miliyan 15 zuwa 20. (Football Insider)

Nottingham Forest ta sallama tayin sama da yuro miliyan 5 da Atletico Mineiro ta yi wa ɗan wasanta na tsakiya Gustavo Scarpa, ɗan Brazil. (Fabrizio Romano)

Brentford, da Crystal Palace da Fulham na sha'awar ɗan wasan Getafe Borja Mayoral, ɗan Sifaniya. (Fichajes)

Chelsea ta cimma yarjejeniya da Darou Salam ta sayen matashin ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Pape Daouda Diong na Senegal mai shekara 17. (90min)

West Ham da Everton na son sayen ɗan bayan Peterborough da tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 21 Ronnie Edwards, a watan Janairu. (Sun)