Arteta ya buƙaci Ramsdale kada ya yi gaggawar yanke hukunci kan zaman sa a Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, Mikel Arteta ya gargaɗi mai tsaron raga na ƙungiyar, Aaron Ramsdale kan cewa kada ya yi gaggawar yanke hukunci game da zaman sa a ƙungiyar.
Hakan na zuwa ne bayan da lamurra ke ƙara taɓarɓare wa Ramdale tun daga farkon kakar wasa ta bana.
Mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ingila, Gareth Southgate dai ya faɗa wa Ramsdale cewa ba zai masa alƙawarin saka shi cikin tawagar Ingilar da za ta buga gasar Euro 2024 ba matuƙar ya ci gaba da cin benci a Arsenal.
Sau bakwai kacal Arsenal ta fara wasa da Ramsdale mai shekara 25 da haihuwa, tun bayan fara kakar wasa ta bana.
Yanzu haka sabon mai tsaron raga na ƙungiyar da aka sayo kwanan nan David Raya shi ne zaɓin farko.
Arteta ya ce Ramsdale na da “muhimmiyar rawar da zai taka” a ƙungiyar (Arsenal).
Lokacin da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar Ramsdale ya sauya ƙungiya a watan Janairu, Arteta ya ce gaggawa “ba aba ce mai kyau ba ko kaɗan.”
“Muna buƙatar kowa da kowa a ƙungiyar nan, kuma Aaron na da muhimmiyar rawar da zai taka.” In ji Arteta.
Kociyan Ingila, Gareth Southgate ya gayyaci Ramsdale domin buga wasanni biyu da Ingilar za ta yi da Malta da kuma North Macedonia a wannan wata.
Southgate ya ce ya tattauna da Ramsdale kan makomarsa a lokacin atisayen da ya gabata.
Kociyan na Ingila ya ce “Har yanzu yana nan yana fafutikar zama zaɓin farko a Arsenal.”
“To amma a zahiri, idan muka shiga watan Maris, kuma ya kwashe wata shida ba tare da buga isassun wasanni ba, to ba zan yi alƙawarin da ba zan iya cikawa ba.”













