Bayern Munich na nazari a kan Solskjaer da Alonso, Man U na zawarcin Tel

Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ole Gunnar Solskjaer
An wallafa

Bayern Munich na son daukar tsohon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer a matsayin kocinta na wucin gadi idan ta yanke shawarar korar Thomas Tuchel. (Sky Germany)

Zakarun na Jamus na kuma tunanin zawarcin kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso, wanda aka danganta da Liverpool. (Athletic - subscription required)

Steve Bruce ya nuna sha’awar zama kocin tawagar kwallon kafar kasar Koriya ta Kudu bayan korar da aka yi wa Jurgen Klinsmann a makon daya gabata sai dai kuma yana cikin jerin sunnayen wadanda aka gabartawar kungiyoyin kwallon kafa ta kasar Saudiyya(Mirror)

Manchester United ta na son ta dauko dan wasan gaban Bayern Munich da Faransa Mathys Tel, mai shekara 18, inda wakilinsa ya amince da cewa dole’’su yi nazari a kan dukanin tayin da aka yi mu su ‘’ a wannan bazara (90min.com)

Kungiyar na kuma zawarcin dan wasan tsakiya na AC Milan da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 25. (Football Transfers)

Chelsea ta na son ta dauko dan wasa mai hari na kungiyar Bologna da Netherlands Joshua Zirkzee, dan shekara 22, sai dai za su fuskanci goggaya daga wasu kungiyoyi da suka hada da Arsenal da Manchester United da kuma Barcelona. (Teamtalk)

Dan wasan tsakiya na Jamus Joshua Kimmich, mai shekara 29 na Shirin barin Bayern Munich a karshen kakar wasani saboda dangantakar da ke tsakaninsa da kocin kungiyar Thomas Tuchel ta yi tsami. (Bild - in German)

Abu ne mai wuya Aston Villa ta mayar da yarjejeniyar aron dan wasan Galatasaray Nicolo Zaniolo ta din-din a bazara yayin da dan wasan tsakiya na Italiya mai shekara 24 na son ya koma Serie A. (Calciomercato - in Italian)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Darektan kwallon kafa na Brentford Phil Giles, da tsohon darektan wasanni na Monaco Paul Mitchell da tsohon manajan Roma Tiago Pinto na cikin wadanda ake ganin za su maye gurbin Dan Ashworth a Newcastle. (The i)

Arsenal na sha'awar dan wasa mai kai hari na Aston Villa da Ingila Ollie Watkins mai shekara 28 (Fichajes - in Spanish)

Gareth Southgate ya sa ido a kan wasu yan wasan tsakiya su uku watau Kobbie Mainoo na Manchester United mai shekara 18 da James Garner na Everton dan shekara 22 da kuma Harrison Reed dan shekara 29 na Fulham – yayin da ya fara shirye -shiryen hada 'yan wasan Ingila a wasan sada zumunci da za a tsakanin kasar da Brazil da Belguim a watan gobe . (Mail)

West Ham ta damu cewa darektan fasahar kungiyar Tim Steidten ba ya jin dadin zamansa a kungiyar kuma watakila zai iya barin kungiyar a karshen kakar wasa. (Guardian)

Ana gab da nada mataimakin kocin Manchester United Eric Ramsey a matsayin kocin Minnesota United a Amurka. (The Athletic - subscription required)

West Ham da Crystal Palace da Southampton na zawarcin dan wasan gaban Sunderland da Ingila Jack Clarke dan shekara 23 wanda an yi kiyasin darajarsa ta kai fam miliyan 23. (Football Insider)