Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
James zai ci gaba da taka leda a Chelsea kaka shida
Mai tsaron bayan tawagar Ingila, Reece James ya saka hannu a kan sabuwar yarjejeniyar da za ta kare a Chelsea a 2028.
Dan kwallon da ya fara daga makarantar matasan Chelsea yana da kwantiragi a Stamford Bridge da zai kare a 2025, wadda ya kulla a Janairun 2020.
James ya fara buga wasan farko a Chelsea a Satumbar 2019 - kawo yanzu ya yi mata karawa 128, wanda ya lashe Champions League a 2021.
Mai tsaron bayan ya buga wasa 87 a Premier League da cin kwallo 7 ya kuma bayar da hudu aka zura a raga.
A kakar nan ta 2022/23, James ya buga karawa biyar a babbar gasar tamaula ta Ingila da cin kwallo daya.
Chelsea tana mataki na shida a teburin Premier bayan buga wasa shida.