Matashin da ya rungumi sana'ar sayar da abinci saboda yajin aikin ASUU

Bayanan bidiyo, Matashin da ya rungumi sana'ar sayar da abinci saboda yajin aikin ASUU
Matashin da ya rungumi sana'ar sayar da abinci saboda yajin aikin ASUU
An wallafa

Wani dalibi a arewacin Najeriya ya ce ya rungumi sana'ar dafa abinci da sayar da shi ne sakamakon yajin aikin da kungiyar malaman Jami'o'i ta ASUU take yi.

ASUU ta kwashe wata bakwai tana yajin aiki bisa abin da ta kira matakin gwamnatin tarayya na kin biya mata bukatunta na inganta ilimi a kasar.

Wannan batu ya sa dalibai sun koma gida kuma galibinsu ba su da aikin yi.

Sai dai Chef Kamal Ahmed, dan asalin jihar Kano kuma dalibi a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya shaida wa BBC cewa ya rungumi sana'ar sayar da abinci gadan-gadan domin ya ga babu alamar janye yajin aikin.

Ya ce ba zai daina sana'ar sayar da abincin ba ko da kuwa ASUU ta janye yajin aikin.