Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi waje da Bayern Munich a gasar DFB Cup
Zakarun Jamus Bayern Munich sun sha mamaki a minti na 96 a wasan da suka buga a gasar DFB Pokal da Saarbrucken wanda ke wasa a rukuni na uku a gasar ƙasar Jamus, inda su ka yi rashin nasara da ci 2-1.
Harry Kane ya kasance a benci amma Bayern ta fara wasan da Thomas Muller da Leroy Sane da kuma Manuel Neuer.
Wannan shi ne karo na uku a cikin shekaru huɗu da Bayern - wadda ta lashe kofin Bundesliga a duka kakannin wasanni 11 da ta wuce - ta fice daga gasar Jamus a zagaye na biyu.
Bayern, wadda za ta ziyarci Borussia Dortmund ranar Asabar, ta kuma rasa ɗan wasan baya na tsakiya Matthijs de Ligt, a farkon wasan, sakamakon raunin da ya samu a gwiwarsa a farkon wasan, wanda ya bar ƙungiyar da ɗan wasan baya guda ɗaya kacal.