Zaben Kenya: Yadda ake samun rabuwar kawuna a yankunan Kenya da suka fi yawan masu zabe

An wallafa

A yankin al’ummar kabilar Kikuyu da ta fi yawan yawan masu jefa kuri’u, ana kara samun bambance-bambance kan matakin da Shugaba Uhuru Kenyatta ya dauka na nuna goyon baya ga tsohon wanda suke gaba Raila Odinga, maimakon mataimakinsa William Ruto, domin ya gaje shi a zaben ranar 9 ga watan Augusta da mutane da dama ke ganin zai yi zafi.

Mista Kenyatta – da ke kare wa’adin mulkinsa na biyu wanda kundin tsarin mulki ya ba shi, an dade ana daukar sa a matsayin jagaba kuma babban dan siyasa na al’ummar ta Kikuyu, inda dattawan al’ummar ke kiransa a matsayin "danmu."

To sai dai bayan ziyarar BBC a lardin Nyeri – da ke makwabtaka da wani tsauni na kasar Kenya – ta fito karara cewa tagomashinsa na raguwa kan matakin da ya dauka na mara wa Mista Odinga baya a wani abu da ya kira hadin kan kasa bayan gabar siyasa ta gomman shekaru.

Wani Lauya, Wahome Gikonyo na ganin Shugaba Kenyatta ya yaudari mataimakinsa Mista Ruto , wanda ya ce ya taimaka masa lashe zabe har sau biyu a kan Raila Odinga.

Mista Gikonyo ya bayyana hakan ne yayin zantawa da BBC a ofishinsa a wani babban lardin kasar Nyeri.

"Ruto ya yi aiki tukuru a 2013 da kuma 2017. Da ba don shi ba, da Kenyatta bai samu nasarar zamantowa shugaban kasa ba. Shin haka ya kamata a saka wa aboki?’’, in ji shi.

Wasu mazauna yankin, kamar Pastor Hannah Kanyithere, na ganin cewa bai kamata Shugaba Kenyatta ya sanya baki kan wanda zai gaje shi.

"Me ya sa shugaban kasa ke daukar bangare a wannan zabe da ke tafe? Idan ba zai goyi bayan mataimakinsa ba, ya kamata ya zamanto dan baruwana,’’ a cewar malamin cocin.

Sai dai wani direban tasi, Hassan Kahoro, ya kare Mista Kenyata, inda ya ce duba da cewa kabilanci na taka rawa a siyasar Kenya, lokaci ya yi da al’ummar Luo za su fitar da shugaban kasa na farko – kuma Mista Odinga.

"Ya kamata mu bai wa al’ummar Luo damar jagorantar wannan kasa. Wa ya ce kujerar shugaban kasa ta zamanto ta al’ummar Kikuyu da kuma Kalenjin?’’ a cewar Mista Kahoro, yayin da yake jawabi gaban dandazon jama’a da suka taru kusa da babbar kasuwar yankin.

Yana Magana ne kan cewa cikin shugabannnin Kenya guda hudu da suka Mulki kasar tun bayan samun yancin kai, uku daga ciki sun fito daga al’ummar Kikuyu.

Marigayi Daniel Arap Moi – wanda ya kasance shugaban kasa mafi dadewa da ya Mulki kasar har na tsawon shekaru 24 – dan kabilar Kalenji ne, in ji Mista Ruto.

Shi ma wani mai sana’ar yin walda, Jackson Maina, ya goyi bayan matakin Mista Kenyatta na mara wa Mista Odinga, mai shekara 77, wanda magoya bayansa ke masa lakabi da ‘Baba’ ko kuma ‘Father’.

"Muna goyon bayan shugaban kasa, don haka muna bayan Baba," a cewarsa yayin da yake tsaye a wajen shagonsa na walda.

An cika garin Nyeri da manyan allunan ‘yan takara da fastoci a daidai lokacin da zaben kasar ke karatowa.

Ba abin da ake ji idan ban da wakokin dukkan 'yan takarar da ke tashi ko ta ina.

Wata waka – da shahararren mawakin kasar Ben Githae ya yi wa Mista Odinga – tana cewa ‘yan Kenya za su tsira a hannun Odinga da mataimakiyarsa Martha Karua – tsohuwar Ministar Shari’a da ta fito daga Kikuyu da kuma ake daukar a matsayin ‘yar kasa’’ na tsaunin Kenya.

Har ila yau, wata waka – ta Betty Maina – na kira ne ga mutane da su fito su kadawa Mista Ruto  kuri’a, wanda shi kuma ya zabi wani dan kasuwa daga al’ummar Kikuyu da ya fito daga lardin Nyeri, Rigathi Gachagua, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki.

Duk da cewa Mista Gachagua ya fuskanci zargin cin hanci da rashawa, amma babban mutumi ne da zai iya jawo hankalin jama’a, kuma yana da goyon bayan ‘yan Kikuyu.

Miss Karua, ‘yar siyasa ce da aka santa ko ta ina – inda aka fi sanin ta a matsayin wacce ke da hankoron ganin an kyautata bangaren shari’a, wacce kuma ba ta lamunci aikata cin hanci da rashawa ba a cikin gwamnati.

Sai dai, idan za a amince da kuri’ar jin ra’ayin da wata cibiyar bincike ta Tifa ta gudanar, ba ita ba, har ma da Mista Kenyatta, ba wanda ya jawo ra’ayin al’ummar Kikuyu na ganin sun zabi Mista Odinga.

Kuri’ar ta nuna Mista Ruto na kan gaba da yawan kuri’u a tsaunin Kenya – inda yake da kashi 66 yayin da Odinga kuma ke da 27.

A matakin kasa baki daya, abin ya sauya, inda Mista Odinga ke gaba da karamin rinjaye, yana da kashi 46.7 yayin da Ruto ke da 44.4 – wanda hakan bai ga mutum ya sami nasarar shugaban kasa ba, inda ake son wanda zai sami nasara ya samu kuri’u sama da kashi 50 domin guje wa shiga zagaye na biyu. 

Don haka, dukkan bangarorin za su yi kokari wajen ganin sun jawo hankalin masu zabe a kwanaki karshe na yakin neman zabe.

Matakin Shugaba Uhuru Kenyatta na mara wa Raila Odinga, ba kan mutanen Kikuyu da ke da yawan kuri'u kadai ta raba ba – har ma da ta iyalansa.

Dan uwansa, Kungu Muigai ya fada wa manema labarai cewa shugaban kasa ya yi watsi da bukatar dattawan Kikuyu ta hanyar kin mutunta yarjejeniyar 2013 da aka cimma, da ke son al’ummar su mara wa dan kabilar Kalenji lokacin da wa’adin mulkin Shugaba Kenyatta karo na biyu zai kare.

Rarrabuwar kawunan har cikin manyan jagororin al’ummar ta Kikuyu, kamar yadda Nduhiu Njama, mai shekara 100, ya bayyana yayin da yake marabtar mu a gidansa da ke yankin Nyeri.

"Mun samu yancin kai ta hanyar hadin kai. Abin da muke gani a yanzu, ta rarrabuwar kawuna, za ta iya jawo mana koma baya,’’ a cewar Njama lokacin da yake nuna wasu hotunansa a baya.

Yawancin mutanen Kikuyu manoma ne da ke noman ganyen shayi da kuma shuke-shuke, da nomar ban-ruwa da kuma kiwon shanu a fadin tsaunin Kenya. 

An gyara yawancin hanyoyin a yankin ta yadda manoma ke samun sauki wajen kai kayan su kasuwa.

BBC ta ziyarci manoma da ke kusa da garin Othaya, wanda ya kasance garin mahaifar marigayi shugaban kasar Mwai Kibaki.

Mun yi kicibis, da George Wambugu, yayin da yake bai wa shanun sa da yake kiwo abinci, inda ya ce yana goyon bayan mista William Ruto.

"Ruto manomi ne kamar ni, sannan a lokacin da yake ministan aikin gona, ya kawo sauye-sauye da suka sanya manoman ganyen shayi samun alfanu da ba a taba samu ba.

Na san cewa zai inganta bangaren aikin gona,’’ a cewar wani mahaifi mai ‘ya’ya uku, inda yake nuna goyon bayansa ga Ruto kamar yadda manomada dama suka yi.

Sai dai, wasu sun ki nuna goyon bayansu ga Ruto – wand kuma hakan baa bun mamaki bane ganin cewa ana kara samun rarrabuwar kawuna.

"Taimakon da muke so kawai shi ne karin taki daga wajen gwamnati domin kara inganta noman ganyen shayi da muke yi,’’ a cewar wata Uwa mai shekara 80 lokacin da take cire ganyen shayi daga gonarta.

Shi kuma shugaban kungiyar manoma ta Othaya, ya ce babu dan takara da yake goyon baya a wannan zabe.

Ya fada wa BBC cewa "Ban damu ba ko kadan a kan wanda zai zama shugaban kasa a ran 9 ga watan Augusta, abin da nake so kawai shi ne kyawawan tsare-tsare da za su kara inganta noman ganyen shayi.